‘Yan Bindiga Sun Kaddamar Da Hari Gonar Obasanjo

Rahotanni daga birnin Abeakuta na Jihar Ogun na bayyana cewar wasu ?an bindiga ?auke da muggan makamai sun kai hari gonar tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta Ota dake Jihar da sanyin safiyar ranar yau.

Rahotanni sun bayyana cewar muggan ‘yan Bindigar sun sace wasu ma’aika a gonar tsohon shugaban dake garin Kobape da ke jihar Ogun.

Rahotanni sun ce maharan sun faki mutanen ne, tare da budewa motarsu wuta, kana daga baya suka yi awon gaba da su.

Ko da yake ba a bayyana sunayen mutanen ba, amma manyan jami’ar katafariyar gonar tsohon shugaban ?asar ne.

Related posts

Leave a Comment