Kano: Gwamnatin Ganduje Ta Hana Wa?o?in Yabon Annabi

Gwamnatin jihar Kano ta ce babu wani sha’iri da zai ?ara wa?ar begen Annabi a jihar sai idan ta ba shi lasisi.

Ta ce ri?on sakainar kashi da ta ga mawa?an na yi da damar da aka ba su ne ya sa ta fito da wa?annan sabbin sauye-sauye.
Shugaban hukumar Isma’il Muhammad Na’abba wanda aka fi sani da Afakallah a wata hira da BBC ya ce, ?imar da ake ganin sha’irai ke da ita a baya ce take neman zubewa, abin da su kuma ba za su bari ba.

An hana wakokin yabon Annabi a Kano sai da izinin gwamnati

Ya sha alwashin cewa duk mutumin da aka kama da irin wa?o?in da ke ta?a matsayin fiyayyen halitta ko kuma wani mai daraja ko Ubangiji da kansa ba za su bari ba sai sun ?auki mataki.

Ga wasu daga cikin sharu??an da dokar ta kunsa:

Babu wani mawa?i da zai ?ara wa?a sai da shaidar lasisin da gwamnati ta ba shi.
Ko da mawa?i na da lasisin izini to sai ya kawo wa?ar ta shi an saurara idan da wani abu da ya ci karo da dokar hukumar a cire shi.
An haramta majalisi a jihar sai da izini daga hukumar, kuma ko da izini an daina yi a cikin wuraren zaman jama’a ko kusa da masallaci ko kuma kusa da kasuwa.

Babu makarantun Islamiyya cikin wannan mataki, saboda suna samun kulawa kai tsaye daga gwamnati ta wasu hanyoyin.
Ba za a yarda da ana majalisi ana ha?a mata da maza ba ko kuma mawa?i ya ri?a rawar shoki ko kuma wani abu makamancin haka.
Afakallah ya ce wa?anda kawai suka yi rijista da hukumarsu ne za su ci gaba da wa?o?in bege a fadin jihar.

Ya kuma ce “Tuni muka nemi gidajen rediyo a Kano su daina sanya irin wa?annan wa?o?i har sai lokacin da muka bayar da izini”.

Related posts

Leave a Comment