Fadan Karshe Da ‘Yan Bindiga: Duk Rintsi Ba Zan Bar Zamfara Ba – Matawalle

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan Bello Matawalle, ya soke duk wata tafiya da zata fitar da shi cikin jihar, dai dai lokacin da aka tsananta hare-hare kan yan bindiga.

Da yake zantawa da kafar watsa labarai ta DW Rediyo, gwamnan yace matakan da aka ?auka kan yan bindiga ya fara haifar da ?a mai ido.

Wane sakamako aka fara samu bayan ?aukar matakai?

Matawalle ya bayyana cewa ?arayi sun fara sako wa?anda suka sace don dole domin ba su iya ciyar da su saboda an toshe musu kafar samun abinci, man fetur da kuma sabis ?in sadarwa.

Yace mutanen da suka shafe makwanni ko watanni a hannun yan bindiga yanzun sun dawo gida, yayin da suka fara zubar da abubuwan hawansu domin babu man fetur.

Wane matakai jami’an tsaro suka ?auka a jihar?

A jawabin gwamnan yace: “Shugaban rundunar sojojin ?asa na cikin jihar mu domin jagorantar Operation ?in jami’ansa. Sojoji da yan bijilanti sun shirya don kutsawa har ma?oyan yan bindiga a cikin jeji.”

“Sojoji na cigaba da tsananta hare-haren, da yardar Allah sai an tarwatsa dukkan sansanonin yan ta’adda ?aya bayan ?aya, kuma muna samun nasara sosai.”

Gwamnan ya kara da cewa duk halin da al’ummar Zamfara suka tsinci kansu bayan datse sabis, shima zai ?an?ani yanayin. “Ba inda zanje, ina cikin Zamfara har zuwa sanda za’a kawo karshen wannan aikin. Nima zan ?an?ani kuncin da datse sabis zai jefa mutanen Zamfara a ciki.”

“Kamar yadda kuke gani, an jibge jami’an tsaro a wuraren bincike duk bayan kilomita biyar a fa?in jihar, domin ba zamu bar wani ?an ta’adda ya tsira ba ko ya samu hanya.

Related posts

Leave a Comment