Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu ya zauna da manyan Maluman Addinin Musulunci domin duba halin tsadar rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki. Rahotanni sun bayyana cewar manyan Malaman ?arkashin jagorancin Shugaban ?ungiyar Izala na ?asa Sheikh Abdullahi Bala Lau, sun shaida wa shugaban irin yanayin da ake ciki a kasar, sannan sun isar masa da sa?on Al’ummar Nijeriya Yayin ganawar ta yammacin Alhamis, Shugaban ?asa Bola Tinubu ya ce masu ?aukar nauyin zanga-zanga mutane ne da suka ?ora masalaharsu…
Read MoreAREWA 24: Ya Zama Dole A Sanya Dokar Ta Baci A Bangaren Gidajen Yada Labarai – Masana
A tattaunawar da masanan suka yi ta cikin shirin gidan talabijin na Liberty mai suna “Democracy In Practice” a turance, sun bayyana ?aukar matakin hakan a matsayin abin da ya wajaba duba da irin halin da ?asa ta tsinci kanta a ciki. Masanan wa?anda suka ha?a da babban sakatare na hukumar gidajen ya?a labarai ta Najeriya (BON) Dr Yemi Bamgbose, sai kuma Dr Emman Shehu daga cibiyar horar da ‘yan Jarida ta ?asa (IIJ) da Malam Sa’idu Carpenter ?wararren dan jarida. Dr Yemi Bamgbose ya koka da irin halin da…
Read MoreTsaro: Sukar Matawalle Da Ribadu Sukar Tinubu Ne – Matasan Arewa
Kungiyar tuntuba ta matasan Arewa (AYCF) ta bayyana cewa ?aukar nauyin sukar ?aramin ministan tsaro Bello Matawalle da babban mai ba shugaban ?asa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, wani yunkuri ne na sukar shugaba Tinubu. Kungiyar ta bayyana cewar a fili yake kwanan nan an ga Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya fito ta kafar talabijin na Channel yana bayyana cewar wai shugaban ya gaza wajen samar da tsaro ba jihar Zamfara da yankin Arewa. Hakazalika Gwamnan Lawal ta hannun kungiyoyin da ya ?auki nauyin su, sun fito suna sukar…
Read MoreTsadar Rayuwa: Tinubu Ya Gargadi Masu Hankoron Gudanar Da Zanga-Zanga
Shugaban ?asa Bola Tinubu ya bu?aci ‘yan ?asar da kada su yi zanga-zangar nuna ?acin rai da matsin rayuwa a wata mai zuwa, kamar yadda Ministan Ya?a Labarai Mohammed Idris ya bayyana. Da yake magana da manema labarai jim ka?an bayan ganawa da shugaban ?asar a yau Talata, ministan ya ce Tinubu ya bu?aci masu shirya zanga-zangar da su dakata tukunna. “Game da maganar zanga-zanga, shugaban ?asa ya ce babu bu?atar yin ta tukunna,” in ji shi. “Ya nemi su jingine batun, ya nemi su jira su ji martanin da…
Read MoreBabu Wata Makarkashiya Da Ake Yi Wa Matatar Man Dangote- Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Najeriya ta fara yun?urin sasanta rikicin sa?anin da aka samu tsakanin matatar mai ta Dangote da kuma hukumomin da ke kula da harkokin man a ?asar. ?aramin Ministan Man Fetur Heineken Lokpobiri ya ce ya jagoranci wani zama da Aliko Dangote shugaban kamfanin Dangote, da Mele Kyari shugaban kamfanin NNPCL, da Farouk Ahmed shugaban hukumar Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA), da Gbenga Komolafe shugaban Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission (NUPRC) a yammacin yau Litinin. “Ganawar wani yun?uri ne na gano maganin matsalolin da matatar ke fuskanta,”…
Read MoreZargin Daukar Nauyin Ta’addanci: Turji Na Da Ciwon Hauka – Bello Matawalle
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Ministan kasa a ma’aikatar tsaron Najeriya Bello Matawalle ya yi watsi da zargin da fitaccen ‘dan ta’adda Bello Turji ya masa na kawar da kai wajen yaki da ta’addanci lokacin da yake rike da kujerar gwamnan Zamfara. Turji ya danganta karuwar ayyukan ‘yan bindiga a jihar da kuma makwabtanta da manufofin gwamnatin Matawalle, inda ya bayyana cewar mazauna Shinkafi da Zurmi da kuma Isa dake Sokoto na da masaniya a kai. A martanin da ya gabatar ta hannun Dayemi…
Read MoreZanga-Zangar Tsadar Rayuwa: Kutungwilar ‘Yan Adawa Ne Da Niyyar Kifar Da Gwamnatin Tinubu – Fadar Shugaban Kasa
Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya zargi magoya bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023 da yunkurin kifar da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu da fakewa da zanga-zangar nuna fushin ?an Najeriya ga matsin rayuwa da ake fama da. Onanuga ya yi wannan zargin ne a cikin wata sanarwa da ya sanya a kan shafinsa sa ta X ranar Asabar. Sai dai bai bayar da wata hujja da za ta tabbatar da zargin…
Read MoreTsohon Gwamnan Zamfara Matawalle Na Da Hannu A Ta’addanci – Bello Turji
Shahararren shugaban ‘yan ta’adda, Bello Turji ya zargi karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da hannu wajen tallafawa ta’addanci a Najeriya. Bello Turji Kachalla, wanda aka fi sani da Turji, sanannen dan ta’adda ne kuma shugaban ‘yan fashi da makami wanda ya yi ta kai hare-hare a jihohin arewacin Najeriya da suka hada da Zamfara, Sokoto da Niger. Ana zargin shugaban ‘yan ta’addan mai shekaru 28 da haihuwa ya jagoranci wasu ‘yan bindiga daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Janairun 2022, inda ‘yan bindiga suka kashe sama da mutane 200…
Read MoreGwamnatin Delta Ta Janye Aniyarta Na Korar ‘Yan Arewa Daga Jihar
A yanzu haka dai hankalin ‘yan arewacin Najeriya mazauna garin Abavo da ke jihar Delta ya kwanta, biyo bayan janye wa’adin da ake zargin masarautar garin ta ba su na kwanaki hudu da su fice daga garin, saboda yawaitar matsalar sace-sacen jama’a da ta addabi yankin. Janyewar wannan wa’adi dai ta biyo bayan kwarmata lamarin da ‘yan arewar suka yi a sashen Hausa na BBC, abin ya kai ga kunnen fadar shugaban Najeriyar, da gwamnan jihar ta Delta, da shugaban ?aramar hukumar Ika ta Kudu, da Ha?akar ?ungiyoyin kare fararen…
Read MoreMajalisa Za Ta Binciki Ingancin Man Fetur Da Ake Sha A Najeriya
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Hon. Tajudeen Abbas ya ce majalisar za ta gudanar da cikakken bincike kan ingancin man da masu ababen hawa ke amfani da shi a fa?in ?asar. Hon Tajudeen ya bayyana hakan ne a yau Asabar yayin wata ziyara da ya jagoranci shugabannin majalisar wakilan ?asar zuwa matatar mai ta Dangote da ke birnin Legas, kamar yadda Gidan talbijin na Channel ya ruwaito. Kakakin majalisar na wannan maganar ne bayan gwajin ingancin man disel da aka yi a gabansu lokacin ziyarar tasu zuwa matatar. Tun da farko…
Read MoreZanga-Zangar Tsadar Rayuwa: Ba Alfanu Bane Za Mu Kaucewa Faruwar Haka – Fadar Shugaban Kasa
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ?arkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu ta gargadi Matasa masu aniyar shiga zanga-zangar tsadar rayuwa da cewa su dakata domin ba alfanu bace ga ?asar. Ministan ya?a labarai Mohammed Idria ne ya bayyana hakan lokacin da yake tsokaci dangane da shirin da wasu gungun jama’a ke yi na shirya zanga-zanga a ?arshen wata, a wata zantawa da ya yi da gidan rediyon BBC Hausa. Mohammed Idria ya ?ara da cewa Gwamnatin tarayya ta yi kyakkyawan tanadi na…
Read MoreTsadar Rayuwa: Gamayyar Kungiyoyin Arewa Sun Ba Tinubu Wa’adin Mako Guda
Gamayyar ?ungiyoyin arewacin Najeriya ta CNG, ta bai wa shugaban ?asar Ahmed Bola Tinubu wa’adin mako guda da ya hanzarta tare da yin nazari game da halin da al’ummar ?asar ke ciki, tare da ?aukar matakan gaggawa da za su kawo wa ?an Najeriyar sau?in rayuwa. ?ungiyar dai ta ce dole ce ta sa daukar wannan mataki sakamakon yadda ake ci gaba da fuskantar matsin rayuwa musaman tashin farashin kayayyaki a ?aukacin fa?in ?asar. Gamayar ?ungiyoyin arewacin ta Najeriya ta ce, lamarin ?angin da ake fama da shi a ?asar…
Read MoreAn Gano Tulin Muggan Makamai A Jos Babban Birnin Jihar Filato
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun gano makamai masu yawa na zamani da kuma ?irar gida a gundumar Fann da ke yankin ?aramar hukumar Barikin Ladi a jihar Filato. Cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar sun ce sun ?addamar da samame a ?auyukan gundumar ne bayan da wasu ?ata-gari suka kashe wani jami’in shige da fice a lokacin da jami’an tsaro ?ar?ashin rundunar Operation SAFE HAVEN ke sintiri a yankin. An ce ?ata-garin sun kashe jami’in a lokacin da yake duba motarsu wadda aka yi zargin sun ?auko…
Read MoreKano: An Fara Shari’ar Matashin Da Ya Banka Wa Mutane Wuta A Masallaci
Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa, Wata babbar kotun shari’ar Musulunci ta karanta wa Shafi’u Abubakar matashin da ake zargi da cinna wa mutane wuta a masallaci tuhume-tuhume guda hu?u da ake yi masa wa?anda suka ha?a da; Zargin sanadiyyar kisan mutum 23 da gangan ta hanyar cinna musu wuta a masallaci a garin Gadan wanda aka fi sani da Larabar Abasawa cikin ?aramar hukumar Gezawa. Yun?urin kisan wasu mutum biyu a ranar 15 ga watan Mayu 2024 a garin Gadan. Raunata wasu mutane ta hanyar…
Read MoreDalibai Za Su Fara Cin Gajiyar Bashin Karatu A Makon Gobe
?aliban manyan makarantun gwamnatin tarayya a Najeriya da suka nemi bashin ku?in karatu za su fara samun ku?in nan da mako ?aya, a cewar asusun ba da bashin ?aliban. Sai dai shugaban asusun, Akintunde Sawyerr, ya ce ?aliban makarantun da za su fara sabon zangon karatu ne kawai za su ga ku?in a asusunsu a yanzu. A jiya Laraba ne Shugaban ?asa Bola Tinubu ya ?addamar da asusun mai suna Nigerian Education Loan Fund (Nelfund) a hukumance a fadar shugaban ?asa da ke Abuja. Mista Sawyerr ya ce jimillar ?alibai…
Read MoreKarancin Albashi: Kungiyar Kwadago Ta Amince Da Tayin N70,000 Da Tinubu Ya Yi
Shugabannin ?ungiyar ?wadago ta NLC sun sanar da amincewarsu da naira 70,000 a matsayin albashi mafi ?an?anta ga ma’aikatan ?asar. Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne ya amince da sabon albashin a ganawarsa da wakilan ?ungiyoyin ?an ?wadago na ?asar a ranar Alhamis. Wannan na zuwa ne bayan kwashe tsawon lokaci ana ta?addama tsakanin ?an ?wadago da gwamnatin Najeriya game da sabon albashin mafi ?an?anta ga ma’aikata. Shugaban NLC Joe Ajaero ya ce sun amince ne da tayin N70,000 saboda akwai abubuwan da ke ?unshe da ya kira na ?arfafa guiwa.…
Read MoreTsadar Rayuwa: ‘Yan Majalisar Wakilai Sun Sadaukar Da Rabin Albashinsu Na Wata Shidda
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ?an majalisar wakilan Najeriya sun amince da a zabtare kaso 50 na albashinsu na tsawon watanni shida a wani mataki na nuna tausayawa ga yanayin matsin tattalin arzi?i da yunwa da ?an Najeriya ke ciki a halin yanzu. Wannan dai ya biyo bayan amincewa da gyaran ga bu?atar da mataimakin shugaban majalisa, Benjamin Kalu ya yi na bu?atar ?an majalisar da su sadaukar da kaso 50 na albashin nasu na naira 600,000 da suke kar?a. Hon Benjamin Kalu ya…
Read MoreMahaifiyar Mawaki Rarara Ta Shaki iskar ‘Yanci
Mahaifiyar shahararren mawa?in Hausa Dauda Kahutu Rarara, ta ku?uta daga hannun ?an bindiga bayan shafe mako uku a hannunsu. Mawa?in ne ya tabbatar da sakin Hajiya Hauwa’u Adamu a wani sa?o da ya wallafa a shafinsa na Instagram da safiyar yau Laraba. An sace dattijuwar ne ranar 28 ga watan Yuni a ?auyen Kahutu da ke ?aramar hukumar Danja ta jihar Katsina. “Cikin yarda da Amincin ubangiji, mun samu dawowar mama cikin aminci,” in ji shi. “Ina matu?ar godiya ga unbangijina.” Kawo yanzu dai babu cikakken bayani game da ko…
Read MoreSukar Tinubu: Majalisar Dattawa Ta Tsige Sanata Ndume Daga Matsayinsa
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Majalisar dattawa ta cire Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume daga mu?amin mai tsawatarwa. Majalisar ta ?auki wannan mataki ne a yau Laraba bayan ?orafi da jam’iyyar APC, mai mulki ta yi kan wasu kalaman sanatan a baya-bayan nan. Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanto wata wasi?ar ?orafi daga shugaban jam’iyyar APC na ?asa, Dr Abdullahi Umar Ganduje da kuma sakatarenta, Sanata Bashir Ajibola. Wasi?ar ta zargi Sanata Ndume da furta wasu kalamai wa?anda ke…
Read MoreAsusun Bada Lamuni (IMF) Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Najeriya
Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya rage hasashen da ya yi a kan bun?asar tattalin arzikin Najeriya na 2024 zuwa kashi 3.1. Wannan na ?unshe ne a cikin sabon rahoton asusun a kan tattalin arzikin duniya na watan Yulin 2024, wanda aka wallafa a ranar Talata. IMF ya ce an samu wannan koma baya ne saboda rashin bun?asar tattalin arzikin a zangon farko na wannan shekarar. A bisa sabon hasashen, an samu raguwar kashi 0.2 a bun?asar tattali arzikin Najeriya, wanda a baya aka yi hasashen zai tashi…
Read More



