Kano: An Fara Shari’ar Matashin Da Ya Banka Wa Mutane Wuta A Masallaci

IMG 20240719 WA0112

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa, Wata babbar kotun shari’ar Musulunci ta karanta wa Shafi’u Abubakar matashin da ake zargi da cinna wa mutane wuta a masallaci tuhume-tuhume guda hu?u da ake yi masa wa?anda suka ha?a da;

  • Zargin sanadiyyar kisan mutum 23 da gangan ta hanyar cinna musu wuta a masallaci a garin Gadan wanda aka fi sani da Larabar Abasawa cikin ?aramar hukumar Gezawa.
  • Yun?urin kisan wasu mutum biyu a ranar 15 ga watan Mayu 2024 a garin Gadan.
  • Raunata wasu mutane ta hanyar watsa musu fetur a masallaci lamarin da ya yi sanadin haifar musu da munanan raunika.
  • ?one masallaci da abubuwan da suke ciki al?alin kotun Ustaz Halhalatul-khuza’i Zakaria ya tambayi Shafi’u Abubakar wanda ake tuhuma ko ya fahimci tuhumar sai ya amsa da cewa “E” ya fahimta tare da tabbatar da cewa “lalle haka abin yake ya aikata”.

Babbar kotun Shari’ar MusUluncin ta ?age zamanta zuwa ranar 1 da 2 ga watan gobe na Agustar 2024, inda ake fatan kotun zata yi masa hukuncin kamar yadda masu kara suka nema.

Related posts

Leave a Comment