Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Majalisar dattawa ta cire Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume daga mu?amin mai tsawatarwa.
Majalisar ta ?auki wannan mataki ne a yau Laraba bayan ?orafi da jam’iyyar APC, mai mulki ta yi kan wasu kalaman sanatan a baya-bayan nan.
Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanto wata wasi?ar ?orafi daga shugaban jam’iyyar APC na ?asa, Dr Abdullahi Umar Ganduje da kuma sakatarenta, Sanata Bashir Ajibola.
Wasi?ar ta zargi Sanata Ndume da furta wasu kalamai wa?anda ke iya zubar da ?imar gwamnati da kuma karya gwiwar masu son shigowa ?asar domin zuba jari.
Bayan karanta wasi?ar ne Sanata Akpabio ya nemi a ka?a ?uri’a domin amincewa ko watsi da bu?atar kuma daga ?arshe sanatocin suka za?i tsige Ndume.
Haka nan kuma majalisar ta cire Ndume daga mu?aminsa na mataimakin shugfaban kwamitin kasafin ku?i na majalisar.
Majalisar ta ce a yanzu an mayar da sanatan zuwa kwamitin harkokin yawon sha?atawa.
Nan take kuma aka za?i Sanata Tahir Munguno domin maye gurbin Sanata Ali Ndume.
Ali Ndume, sanata ne wanda ya yi ?aurin suna wajen sukar manufofin gwamnati, yayin da magoya bayansa ke masa kallon mai fa?in albarkacin bakinsa ba tare da tsoro ba.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da Majalisar Dattijan Najeriyar ta dakatar da wani wakili na ta ba.
Ko a watan Maris ?in 2024 majalisar ta dakatar da Sanata Abdul Ningi mai wakiltar maza?ar Bauchi ta tsakiya daga majalisar bayan zargin sa da furta “kalamai da ke iya zubar da ?imar majalisar.”
Majalisar ta ?auki matakin ne bayan wata tattaunawa da sanatan ya yi da kafar yada labarai ta BBC, inda ya yi zargin cushe a cikin kasafin kudin ?asar.
