Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ?arkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu ta gargadi Matasa masu aniyar shiga zanga-zangar tsadar rayuwa da cewa su dakata domin ba alfanu bace ga ?asar.
Ministan ya?a labarai Mohammed Idria ne ya bayyana hakan lokacin da yake tsokaci dangane da shirin da wasu gungun jama’a ke yi na shirya zanga-zanga a ?arshen wata, a wata zantawa da ya yi da gidan rediyon BBC Hausa.
Mohammed Idria ya ?ara da cewa Gwamnatin tarayya ta yi kyakkyawan tanadi na inganta rayuwar al’ummar kasar, kuma nan bada jimawa kowa zai shaida haka, saboda gaka jama’a su ?ara ha?uri.
‘Yan Majalisa Sun Fara Ro?on Matasan Najeriya Da Su Janye Muradunsu Na Yin Zanga Zanga
A cewar mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, tabbas tsare-tsaren gwanatin Shugaba Tinubu sun saka mutane a wahala da yunwa kuma korafin da ‘yan Najeriya suke yana kan tsari amma duk da haka ya ro?i matasan kada su yi zàngà-zàngà irin ta ‘yan kasar Kenya.
