Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Gana Da Manyan Malaman Musulunci

FB IMG 1721978789119~2

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu ya zauna da manyan Maluman Addinin Musulunci domin duba halin tsadar rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki.

Rahotanni sun bayyana cewar manyan Malaman ?arkashin jagorancin Shugaban ?ungiyar Izala na ?asa Sheikh Abdullahi Bala Lau, sun shaida wa shugaban irin yanayin da ake ciki a kasar,  sannan sun isar masa da sa?on Al’ummar Nijeriya

Yayin ganawar ta yammacin Alhamis, Shugaban ?asa Bola Tinubu ya ce masu ?aukar nauyin zanga-zanga mutane ne da suka ?ora masalaharsu sama da ta ?asar.

Jagoran Malaman, Sheikh Bala Lau ya ce za su ci gaba da taimaka wa ?asar da addu’o’i da kuma wayar da kan mutane.

Anasa ?angaren fitaccenmalamin addinin Musulunci kuma shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce sun yi abin da ya dace a kan batun zanga-zangar da ake shirin yi a ?asar, ta hanyar ganawa da shugabanni da gaya musu abin da ya kamata su yi da kuma gaya wa matasan ma abin da ya kamata su yi.

A sa?on da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a ranar Alhamis, Sheikh Daurawa ya ce “Idan wani abu ya faru, to ?ayan biyu ne, ko dai shugabannin ba su yi abin da ya kamata ba, ko matasan ba su yi ba.”

Related posts

Leave a Comment