Mahaifiyar Mawaki Rarara Ta Shaki iskar ‘Yanci

FB IMG 1721198220220

Mahaifiyar shahararren mawa?in Hausa Dauda Kahutu Rarara, ta ku?uta daga hannun ?an bindiga bayan shafe mako uku a hannunsu.

Mawa?in ne ya tabbatar da sakin Hajiya Hauwa’u Adamu a wani sa?o da ya wallafa a shafinsa na Instagram da safiyar yau Laraba.

An sace dattijuwar ne ranar 28 ga watan Yuni a ?auyen Kahutu da ke ?aramar hukumar Danja ta jihar Katsina.

“Cikin yarda da Amincin ubangiji, mun samu dawowar mama cikin aminci,” in ji shi. “Ina matu?ar godiya ga unbangijina.”

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani game da ko an biya ku?in fansa kafin sakin nata.

Related posts

Leave a Comment