Karancin Albashi: Kungiyar Kwadago Ta Amince Da Tayin N70,000 Da Tinubu Ya Yi

Shugabannin ?ungiyar ?wadago ta NLC sun sanar da amincewarsu da naira 70,000 a matsayin albashi mafi ?an?anta ga ma’aikatan ?asar.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne ya amince da sabon albashin a ganawarsa da wakilan ?ungiyoyin ?an ?wadago na ?asar a ranar Alhamis.

Wannan na zuwa ne bayan kwashe tsawon lokaci ana ta?addama tsakanin ?an ?wadago da gwamnatin Najeriya game da sabon albashin mafi ?an?anta ga ma’aikata.

Shugaban NLC Joe Ajaero ya ce sun amince ne da tayin N70,000 saboda akwai abubuwan da ke ?unshe da ya kira na ?arfafa guiwa.

?ungiya ta ce abin da ya ?ara ?arfafa mata guiwa na amincewa da tayin shi ne al?awalin da shugaban ?asar ya ?auka na sake duba albashin duk bayan shekara uku maimakon shekara biyar, kamar yadda mataimakin shugaban Kabiru Adamu Minjibir ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban ?asa.

“Sannan gwamnati za ta bayar da manyan bas bas masu ?aukar mutum 100 wanda zai rage wa ma’aikata wahalar tafiye-tafiye,” in ji shi.

Tun janye tallafin mai da gwamnatin Bola Tinubu ta yi, ta shiga takun-saka da ?ungiyoyin ?wadago, inda suka nemi ?arin albashi da ya zarta kashi 300 cikin 100 sakamakon tsadar rayuwa da janye tallafin ya jefa ?an Najeriya.

Related posts

Leave a Comment