Ofishin Kula da Basussuka na ?asa (DMO) ya bayyana cewa ?ididdigar basussukan da ake bin Najeriya zuwa watan Maris ya kai Naira tiriliyan 121.67, watau kwatankwacin Dalar Amurka biliyan 91.46 kenan.
Babban Daraktan Hukumar DMO, Patience Oniha ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a, a cikin wata sanarwar da ta fitar a Abuja.
Oniha ta ce wannan tulin bashi ya ha?a da wanda ake bin gwamnatin tarayya da kuma jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja.
Ta ce zuwa watan Maris, adadin basussukan cikin gida da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 65.65, yayin da basussuka na waje sun kai Naira tiriliyan 56.02.
Ta ?ara bayyana cewa bashin ya ?aru ne sosai saboda basussukan cikin gida da aka ciwo domin cike gi?in kasafin 2024, sai kuma tashin gwauron zabin da Dala ta ri?a yi, I a kuma Naira darajar ta na karyewar.
