Gumurzun Boko Haram Da ISWAP Ya Bar Tulin Gawarwaki

Rahotannin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar an yi wata arangama tsakanin Kungiyar Boko Haram da tsagen kungiyar karkashin ISWAP. Rahotanni sun bayyana cewar lamarin fafatawar ya yi sanadiyyar mutuwar manyan kwamandoji daga ?angaren kungiyoyin ta’addan biyu masu gaba da juna. Majiyarmu ta Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne tsakanin Dikwa da Bama da ke jihar Borno. Wata majiyar tsaro ta ce Kwamandojin Boko Haram da tawagarsu na kan aikata fashi da makami, lokacin da mayakan ISWAP din a kan…

Read More

Kama Tukur Mamu Ba Zai Shafi Ceto Sauran Fasinjoji Ba – Fadar Shugaban Kasa

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ta ce kama Tukur Mamu, mai shiga tsakani a kokarin sakin fasinjojin jirgin kasan da aka sace, ba zai kawo cikas ga yunkurin da gwamnatin kasar ke yi na kubutar da sauran fasinjojin da suka rage a hannun ‘yan bindiga ba. Ministan kula da harkokin ‘yan sanda na kasar Mohammed Maigari Dingiyadi ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron majalisar tsaro ta kasa da aka yi a Abuja ranar Alhamis. “Ina ganin masu maganar sun…

Read More

Fitinar ‘Yan Bindiga: Mata A Gombe Sun Yi Zanga-Zanga

Labarin dake shigo mana daga jihar Gombe na bayyana cewar wasu matan daga garin Filiya, a karamar hukumar Shongom ta Jihar a ranar Laraba sun yi zanga-zangan lumana bayan kisan da ake zargin makiyaya suke yi wa mazan su. Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Gombe ta tabbatar an kashe mutum 11 sannan an kona gidaje 11 a harin baya-bayan nan a Kushi. Matan da suka yi zanga-zangan sun rufe hanyar zuwa garin suna cewa sun aikata hakan ne don nuna damuwa, sun kuma ce ba su gamsu da matakan…

Read More

Tsaro A Arewa: Gwamnoni Sun Yi Kiran Samar Da ‘Yan Sandan Jihohi

Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya 19 da sarakunan gargajiya a yankin sun yi kira da a yi garambawul ga kundin tsarin mulki na 1999, don samar da yan sandan jihohi. BBC ta rawaito cewa, a cewarsu wannan ne kadai zai sa a shawo kan matsalar tsaro da yankin ke fama da ita dama kasa baki daya. Yankin Arewacin na Najeriya ya jima yana fama da matsalar yan fashin daji, da satar mutane don neman kudin fansa, da sauran nau’o’in ayyukan ta’addanci. Kungiyar gwamnonin arewa ta NGF, da ta sarakunan gargajiya (NTRC)…

Read More

Kaduna: Dakarun Soji Sun Tarwatsa Sansanin ‘Yan Bindiga

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Dakarun rundunar sojoji na 1 Division sun yi nasarar halaka ‘yan bindiga tare da kama wasu da dama a ranar Litinin. Mai magana da yawun rundunar sojoji, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da lamarin cikin sanarwar da ya fitar a shafin Twitter na rundunar a ranar Talata. A cewar sanarwar, GOC na 1 Division, Nigerian Army, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ne ya jagoranci tawagar da ta kai samamen tare da hadin gwiwan wasu kwamandoji. Nwachukwu ya ce: “Dakarun sojoji…

Read More

Alaka Da ‘Yan Ta’adda: Kotu Ta Bada Umarnin Cigaba Da Tsare Tukur Mamu

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata kotu da ke birnin ta ba wa hukumar tsaron cikin gida ta DSS, damar ci gaba da tsare mai shiga tsakanin ‘yan Bindiga Tukur Mamu har na tsawon sama da kwanaki 60. Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Talata, bayan da lauyan hukumar ta DSS ya bukaci hakan. A cikin wata takarda da ta gabatar wa kotun, hukumar tsaron ta DSS ta bukaci kotun ta ba ta damar ci gaba da tsare Tukur Mamu, ne domin…

Read More

Akwai Sauran ‘Yan Matan Chibok A Hannun Boko Haram – Rundunar Soji

Rundunar sojin Najeriya tace yanzu haka dalibai mata daga Sakandaren Chibok da mayakan Boko Haram suka sace a shekarar 2014, 98 ne ke tsare a hannun ‘yan ta’addan daga cikin 276 da suka kwashe. Shugaban sashen kula da leken asiri na rundunar hadin kan dake yaki da yan ta’adda a arewa maso gabashin Najeriya da ake kira ‘Operation Hadin Kai’, Kanar Obinna Ezuipke ne, ya sanar da adadin ga manema labarai a Maiduguri. Ezuipke yace daga cikin ‘yan matan 276 da aka sace, 57 sun tsere daga hannun mayakan a…

Read More

Borno: Zulum Ya Dauki Nauyin Iyalan Shugaban ‘Yan Sa Kai Da Aka Kashe

Rahotannin daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana Gwamna Babagana Zulum na Jihar ya bada kyautar gida da Naira miliyan 10 ga iyalan tsohon kwamandan yan sa kai na civilian JTF, Babagana Tela, wanda Boko Haram suka kashe. Mista Tela wanda aka fi sani da ‘Kadau’ saboda jarumtarsa shine kwamandan JTF a Bama, daya daga cikin garuruwan da aka kwato a Borno daga hannun maya?an Boko Haram. Sanarwar da Isa Gusau, mashawarcin Gwamna Zulum a bangaren watsa labarai ya fitar ta ce gwamnan wanda ya ziyarci iyalan mamacin ya…

Read More

Kamun Da DSS Ta Yi Wa Tukur Mamu Ta’addanci Ne – Gumi

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Shahrarren Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kira ga Hukumar tsaron farin kaya, DSS, ta gaggauta sakin Tukur Mamu ko ta kai shi kotu. Gumi ya bayyanawa gwamnati cewa dokar kasa bata amince a rike mutum sama da kwana guda ba’a kai shi kotu ba, ri?e mutum sama da haka karan tsaye ne da ta’addanci ga dokokin ?asa. A zaman karatun littafin Muktasarul-Khalil da Malamin ke yi mako-mako a Masallacin Sultan Bello dake Kaduna, Gumi yace wannan jarabawa…

Read More

Mun Bankado Makudan Kudade Da Kayayyakin Sojoji A Gidan Tukur Mamu – DSS

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Hukumar DSS ta bayyana cewa ta bankado abubuwa da dama a gidan mutumin dake cinikin kudaden fansan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da yan bindiga suka sace wato Tukur Mamu. Daga cikin abubuwan da suka gano akwai kayan Sojoji, makudan kudaden kasashe daban-daban da sauran wasu muhimman abubuwa. Kakakin Hukumar, Peter Afunanya, ya bayyana hakan jim ka?an bayan kammala binciken kwa-kwaf da Jami’an hukumar suka yi a gidan Tukur Mamu dake Kaduna. Afunanya yace abubuwan da suka bankado na da ban…

Read More

Da Dumi-Dumi: An Fara Bankado Zunubban Tukur Mamu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu majiyoyin tsaro sun ce baya ga alaka da ‘yan ta’addan Najeriya, Tukur Mamu ya shiga hannun hukuma ne saboda alakar da yake da ita mai karfin da wata kungiyar ta’addanci a yankin Sinai dake Misra. Sinai Peninsula yankin arewa maso gabas ne na Misra da ya hada Isra’ila da Gaza ta gabas. Kamar a Najeriya, duk da raguwar yawan hare-haren ta’addanci, ‘yan ta’addan suna nan a yankin kuma sun zama babbar barazana ga jami’an tsaro da sauran Sinai.…

Read More

Ban San Dalilin Da Ya Sa Aka Kama Tukur Mamu – Dr Gumi

Labarin da muke samu daga jihar Kaduna na bayyana cewar Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, yace bashi da wani bayani kan dalilin da yasa aka damke hadiminsa, Malam Tukur Mamu a birnin Alkahira na kasar Misra. “Yanzu nake jin cewa an tsare shi a birnin Alkahira da iyalansa. Ban san dalilin faruwar hakan ba kuma nayi mamaki saboda gwamnatin Najeriya bata zargesa da komai ba ko ta ayyana tana nemansa ba.” “Amma na ji cewa ya dawo Najeriya, a don haka neka fatan samun karin bayani bayan isowarsa.”

Read More

Sojin Kundunbala Sun Yi Maganin ‘Yan Bindigar Hanyar Kaduna Zuwa Zariya

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Dakarun sojojin Najeriya sun bindige wasu yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Zaria a karamar hukumar Igabi, ta Jihar Kaduna. Mista Samuel Aruwan, kwamishinan a ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba da ya fitar kuma aka rarrabawa manema labarai a Jihar. “Da shigarsu wurin, sojojin suka fara yi wa yan bindigan ruwan harsashi yayin da yan bindigan suka yi kokarin mayar da martani. An kashe biyu daga cikin…

Read More

DSS Ta Cafke Mai Shiga Tsakanin ‘Yan Bindiga Tukur Mamu Bayan Saukarshi Kano

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar hukumar tsaron farin kaya a DSS, ta tabbatar da cewa an kama mai kamfanin jaridar Desert Herald, wanda kuma yake shiga tsakani don kubutar da fasinjojin jirgin kasa da ‘yan bindiga suka sace daga Abuja zuwa Kaduna. Sanarwar da jami’in yada labarai na hukumar DSS, Peter Afunanya, ya aike wa manema labarai, ta ce ‘yan sandan kasa da kasa na kasar a Masar su ne suka kama Tukur Mamu a filin jirgin sama a birnin Al-khahira ranar 6 ga…

Read More

Da Dumi-Dumi: An Damke Mai Shiga Tsakanin ‘Yan Bindiga Tukur Mamu A Masar

Alhaji Tukur Mamu, jagoran masu sasantawa tsakanin ‘yan bindiga da fasinjojin da aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris, an kama shi a birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar, tare da iyalansa. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Mamu wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin ummara, an tsare shi na tsawon sa’o’i 24 a filin jirgin sama na Alkahira, kuma ana shirin dawo da shi gida Nijeriya. Da ya ke zantawa da Daily Trust, Mamu ya ce…

Read More

Za Mu Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Karshen Shekara – Fadar Shugaban Kasa

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yunkurin da gwamnatin tarayya ke yi na magance matsalar tsaro a kasar, hukumomi sun sha alwashin kawo karshen matsalar daga nan zuwa watan Disamba mai zuwa. Wannan na ?unshe cikin jawabin da ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ya yi lokacin wani taron hadin gwuiwa da wasu takwarorinsa ministoci domin yin karin haske kan matakan da gwamnatin kasar ke dauka don kare al’umma Rauf Aregbesola ya ce ”Babbar manufarmu ita ce mu murkushe su baki daya, sannan mu…

Read More

Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Yi Gaba Da Masallata A Masallacin Juma’a

Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar wasu gungun ‘yan bindiga ?auke da muggan makamai a bisa babura sun kai hari wani masallacin Juma’a dake yankin ?aramar Hukumar Bukkuyum inda suka yi gaba da tarin jama’a. Rahotanni sun bayyana cewar ‘Yan bindigan sun kai farmaki masallacin Juma’a a yankin Zugu dake karamar hukumar Bukkuyum a jihar inda suka sace masu sallah. An gano cewa, ‘yan bindigan sun shiga masallacin tare da tattara jama’a ana dab da fara huduba inda suka shige daji da su.…

Read More

Izala Ta Yi Marhabin Da Korar Sojin Da Suka Kashe Sheikh Goni

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa iqamatis sunnah ta tarayyar Najeriya ta yabawa hukumar sojojin Najeriya wajen zartas da hukunci na kora ga ‘yan ta’addan Sojojin da suka yiwa marigayi Sheikh Gwani Aisami kisan gilla a kwanakin baya a garin Gashua ta jihar yobe. Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, shi yayi wannan furuci a wata takarda da ya fitar ga manema labaru a ofishinsa dake birnin tarayya Abuja. Shehin Malamin yace “zamuci gaba da bibiyar shari’ar da zata gudana a kotu domin ganin an tabbatar da anyi musu shari’ar…

Read More

‘Yan Bindiga Sun Farmaki Babban Kamfani A Kaduna

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar wasu gungun ‘yan bindiga sun farmaki wani kamfanin gona a garin Anchau na karamar hukumar Kubau dake jihar inda suka yi mummunan ta’adi. Rahotanni sun bayyana cewar tsagerun ‘yan Bindigar sun bindige wani soja har lahira tare da yin awon gaba da wasu jami’an kamfanin gonar mutum biyu da misalin karfe 1:30 na ranar Laraba. An tattaro cewa, daya daga cikin wadanda aka sacen wani dan kasar Zimbabwe ne da ke aiki a kamfanin. Wani dan banga da ke aiki…

Read More

Rundunar Soji Ta Kori Sojin Da Suka Kashe Sheikh Goni

Rundunar sojan Najeriya ta kori dakarunta biyu daga aiki wa?anda ake zargi da kashe malamin nan na Jihar Yobe, Goni Aisami, a makon da ya gabata. Sojojin biyu su ne kofur John Gabriel da Adamu Gideon, wa?anda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gabatar ga manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, inda babban wanda ake zargin ya bayyana yadda ya harbe malamin. Mu?addashin kwamandan rundunar 241 Reece da ke Nguru na Jihar Yobe, Laftanar Kanar Ibrahim Osabo, ya fa?a wa manema labarai cewa wani kwamatin ha?in gwiwa ne da aka…

Read More