Alaka Da ‘Yan Ta’adda: Kotu Ta Bada Umarnin Cigaba Da Tsare Tukur Mamu

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata kotu da ke birnin ta ba wa hukumar tsaron cikin gida ta DSS, damar ci gaba da tsare mai shiga tsakanin ‘yan Bindiga Tukur Mamu har na tsawon sama da kwanaki 60.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Talata, bayan da lauyan hukumar ta DSS ya bukaci hakan.

A cikin wata takarda da ta gabatar wa kotun, hukumar tsaron ta DSS ta bukaci kotun ta ba ta damar ci gaba da tsare Tukur Mamu, ne domin samun isasshen lokacin gudanar da bincike.

Tukur Mamu, dai shi ne ya jagoranci karbo da dama daga cikin fasinjojin jirgin kasa wadanda ake zargin kungiyar Ansaru da laifin sacewa, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Abuja babban birnin kasar.

Tun farko dai an kama mawallafin ne a birnin Alkahira na kasar Masar, inda daga baya aka mayar da shi gida Najeriya.

DSS ta sanar da cewa ta kama Mamu ne a kokarin ta na ganin ya amsa tambayoyi kan wasu lamura masu muhimmanci.

Haka nan hukumar ta tabbatar da cewa jami’anta sun gudanar da bincike a gidansa da ke Kaduna in da ta gano wasu kaya da kuma kudade masu dumbin yawa

Related posts

Leave a Comment