Labarin dake shigo mana daga jihar Gombe na bayyana cewar wasu matan daga garin Filiya, a karamar hukumar Shongom ta Jihar a ranar Laraba sun yi zanga-zangan lumana bayan kisan da ake zargin makiyaya suke yi wa mazan su.
Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Gombe ta tabbatar an kashe mutum 11 sannan an kona gidaje 11 a harin baya-bayan nan a Kushi.
Matan da suka yi zanga-zangan sun rufe hanyar zuwa garin suna cewa sun aikata hakan ne don nuna damuwa, sun kuma ce ba su gamsu da matakan da gwamnati ta dauka ba.
“Munyi hakan ne saboda shiru da dagacin garin mu da mahukunta suka yi da kuma rashin kawo karshen rikicin makiyaya/manomaa da ya halaka mazajen mu. Shanun makiyaya sun cinye amfanin gonar mu ba mu da abinci.”
