Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ta ce kama Tukur Mamu, mai shiga tsakani a kokarin sakin fasinjojin jirgin kasan da aka sace, ba zai kawo cikas ga yunkurin da gwamnatin kasar ke yi na kubutar da sauran fasinjojin da suka rage a hannun ‘yan bindiga ba.
Ministan kula da harkokin ‘yan sanda na kasar Mohammed Maigari Dingiyadi ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron majalisar tsaro ta kasa da aka yi a Abuja ranar Alhamis.
“Ina ganin masu maganar sun san Mamu ne kawai ba su san sauran masu sulhu ba tsakanin hukumomi da ?an fashin.
“Akwai mutane da dama da ke sa baki kuma maganganun suna amfani,” in ji Ministan Tsaron, a hirarsa da BBC bayan kammala taron.
Jami’an ‘yan sandan kasa da kasa ne suka kama Tukur Mamu ranar 7 ga watan Satumba a Masar, sannan kuma aka dawo da shi Najeriya bisa umarnin gwamnatin tarayya inda aka mika shi hannun jami’an ‘yan sandan farin kaya na DSS.
Ya ?ara da cewa “Akwai ?an uwan mutanen da hukumomin tsaro da ke shiga tsakani a lamarin. Kama Mamu ba zai kawo ?arshen sulhun ba.”
