Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar wasu gungun ‘yan bindiga ?auke da muggan makamai a bisa babura sun kai hari wani masallacin Juma’a dake yankin ?aramar Hukumar Bukkuyum inda suka yi gaba da tarin jama’a.
Rahotanni sun bayyana cewar ‘Yan bindigan sun kai farmaki masallacin Juma’a a yankin Zugu dake karamar hukumar Bukkuyum a jihar inda suka sace masu sallah.
An gano cewa, ‘yan bindigan sun shiga masallacin tare da tattara jama’a ana dab da fara huduba inda suka shige daji da su.
Har ya zuwa lokacin ha?a rahoton nan babu wani sabon labari daga ?angaren gwamnati akan makomar da wadannan bayin Allah suke ciki.
Jihar Zamfara dai ita ce jiha ?aya tilo a yankin arewa maso yamma inda ‘yan Bindiga suke cin karen su babu babbaka tare da neman gagarar gwamnati da hukumomin tsaro.
