Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu majiyoyin tsaro sun ce baya ga alaka da ‘yan ta’addan Najeriya, Tukur Mamu ya shiga hannun hukuma ne saboda alakar da yake da ita mai karfin da wata kungiyar ta’addanci a yankin Sinai dake Misra.
Sinai Peninsula yankin arewa maso gabas ne na Misra da ya hada Isra’ila da Gaza ta gabas. Kamar a Najeriya, duk da raguwar yawan hare-haren ta’addanci, ‘yan ta’addan suna nan a yankin kuma sun zama babbar barazana ga jami’an tsaro da sauran Sinai.
Mamu ya musanta aikata wani laifi inda yace yana kan hanyarsa ne ta zuwa kasar Saudi Arabia don yin Umra da iyalansa.
An zargi hukumomin Najeriya da nuna halin ko in kula ga wadanda aka sace, lamarin da yasa iyalansu suka dinga neman yadda zasu kubutar da su ko ta wanne hali wanda ya hada da bada kudin fansa.
Wannan ne ya kawo shuhurar Mamu bayan ya fito fili tare da bayyana yadda ya karbo wadanda aka sace daga wurin ‘yan ta’adda duk da ya musanta karbar kudin fansa daga iyalansu ko kai wa ‘yan ta’addan.
Mamu yana cikin jerin wadanda hukumomin tsaron duniya suka sanyawa idanu Wata majiya daga daya daga cikin hukumomin sirri a Najeriya ta ce kamen Mamu ya biyo bayan harkokinsa na ketare ne ba wai kasar Najeriya kadai ba.
“An kama shi a Misra ne saboda bayanansa dake hannun hukumomin tsaron duniya bayan an sanya masa ido a gida da waje jim kadan bayan farmakin jirgin kasa na Kaduna, “Ina tabbatar muku cewa Mamu yana da alaka da manyan kungiyoyin ta’addanci a Misra, ballantana a Sinai zuwa Libya har wasu sassan Afrika ta yamma da kuma gabas ta tsakiya.” – Majiyar tace.
“Ya karbi kudin fansa N2 biliyan na ‘yan ta’adda inda wasu kudin aka biya da dala wanda suka karba daga iyalan wadanda aka sace. Mun dade muna lura da harkokinsa kuma shaidu garemu sosai.”
