Rundunar sojan Najeriya ta kori dakarunta biyu daga aiki wa?anda ake zargi da kashe malamin nan na Jihar Yobe, Goni Aisami, a makon da ya gabata.
Sojojin biyu su ne kofur John Gabriel da Adamu Gideon, wa?anda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gabatar ga manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, inda babban wanda ake zargin ya bayyana yadda ya harbe malamin.
Mu?addashin kwamandan rundunar 241 Reece da ke Nguru na Jihar Yobe, Laftanar Kanar Ibrahim Osabo, ya fa?a wa manema labarai cewa wani kwamatin ha?in gwiwa ne da aka kafa tsakanin ‘yan sanda da sojoji ya kama su da laifin.
Ya ce an kori sojojin ne kan tuhuma biyu da suka ?unshi gazawa wajen gudanar da aikinsu da kuma ?ata sunan aikinsu.
Kanar Osabo ya ?ara da cewa za a mi?a su ga ‘yan sanda a birnin Damaturu don gurfanar da su a gaban kotu.
