Shirin Kawancen Atiku Da Peter Obi Ba Barazana Bane – Fadar Shugaban Kasa

IMG 20240520 WA0040

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa fadar shugaban kasa ta yi watsi da shirin kulla kawance tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi. A cewar fadar shugaban kasa, shugaban kasa Bola Tinubu bai damu da wannan kawancen da ake shirin yi ba, ganin cewa shugaban kasa ba ya barci. A makon da ya gabatane dai ?an takarar shugabancin kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi ya ziyarci wasu jiga jigan jam’iyyar adawa ta PDP domin daura ?amarar fuskantar za?en…

Read More

Najeriya Ta Rasa Makama Tun Bayan Rantsar Da Tinubu – Babachir Lawal

IMG 20240519 WA0133

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Injiniya Babachir Lawal ya yi magani kan kamun ludayin gwamnatin Bola Tinubu. Babachir ya ce tun bayan hawan Tinubu karagar mulkin Najeriya ta ruguje ta rasa madafa. Tsohon sakataren ya ce cire tallafin mai shi ne babban kuskuren da Tinubu ya yi tun kafin nadin mukamai a gwamnatin. Na hannun daman tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana haka yayin hira da gidan talabijin na Trust. Har ila yau, Babachir ya ce sanar da cire tallafin shi ne ya jefa jama’ar kasar cikin mummunan yanayi da…

Read More

Mun Yi Nasara Kan ‘Yan Bindiga Da Kashi Saba’in Cikin Dari – Gwamnan Katsina

Gwamnan jihar Katsina Mallam Dikko Ummaru Radda, ya ce gwamnatinsa ta yi nasarar rage yawan ta’addancin ‘yan bindiga da kashi 70 cikin dari a cikin shekara daya da ta gabata. Gwamnan ya ce an samu wannan nasara ne a sakamakon abin da ya kira kyakkyawan hadin kai tsakanin jami’an tsaro na sa-kai na jihar da kuma jami’an tsaro na kasar. Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, da ya ruwaito labarai ya ce, gwamnan ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Yola babban birnin jihar Adamawa, a yau Asabar a ziyarar…

Read More

An Shawarci Tinubu Ya Yi Amfani Da Karfin Iko Wajen Kafa ‘Yan Sandan Jihohi

IMG 20240226 WA0252

Kungiyar kishin kabilar Yarabawa zalla ta Afenifere, ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya da ya yi amfani da ikonsa ya bayar da umarnin kafa rundunar ‘yansandan jihohi da ta kananan hukumomi. Sakataren yada labarai na kungiyar, Jare Ajayi, ne ya fitar da sanarwar da ke dauke da kiran yau Asabar, a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito. Sanarwar ta ce, kungiyar ta yi kiran ne sakamakon rahotannin da ake ta samu na karin hare-haren ‘yan bindiga da satar jama’a a jihohin Ogun da…

Read More

Najeriya Za Ta Yi Bankwana Da Sayo Mai Daga Waje A Watan Yuni – Dangote

images (41)

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Matatar man Dangote da ke jihar Legas ta ce kasar za ta daina sayen man fetur daga waje a watan Yuni, lokacin da matatar za ta fara aiki. Mai matatar, Alhaji Aliko Dangote shi ne ya bayyana haka a taron kolin shugabannin kamfanoni na Afirka ranar Juma’a a Kigali, babban birnin Rwanda. Hamshakin attajirin ya ce, matatar za ta samar da man da ake bukata a cikin gida ba ga Najeriya ba kadai har ma da sauran kasashen yankin…

Read More

Gwamnatin Buhari Ce Mafi Muni A Tarihin Najeriya – SDP

Muhammadu Buhari, President of the Federal Republic of Nigeria (cropped3)

Shugaban jam’iyyar SDP na Najeriya, Shehu Gabam ya zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da ta gabata da rashin magance matsalolin Najeriya, lamarin da ya ce ya haifar wa gwamnati mai ci fusknatar tarin matsalolin tattalin arziki. Yayin wata hira a shirin ‘Politics Today’ na gidan Talbijin na Channels, Gabam ya zargi gwamnatin Buhari da gazawa wajen magance matsalolin ?asar. ”Na sha fa?a a lokuta da dama cewa gwamnatin Buhari ita ce gwamnati mafi munin gwamnati da aka ta?a gani na tarihin Najeriya, mulkinsa ne ya gadar wa gwamnatin Bola Tinubu matsin…

Read More

Amurka: Malamar Makaranta Dake Lalata Da Dalibai Ta Shiga Hannu

IMG 20240518 073810

Wata kotu a birnin Manchester ta samu wata malamar makaranta da laifin yin lalata da wasu ?alibanta maza guda biyu. An samu Rebecca Joynes, mai shekara 30, da laifukan lalata da ?ananan yaran har sau bibbiyu kowannesu. An shaida wa al?alin cewa hukumar makarantar ta kori malamar, saboda yin lalata da yaro na farko, sai kuma ta sake yi da yaro na biyu a lokacin da ake tsaka da tuhumarta. Malama Joynes ta samu juna-biyu sakamakon lalata da yaron na biyun duk da cewa yana da ?ananan shekaru. Malamar ta…

Read More

Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Ba Kananan Hukumomi’Yancin Kai

IMG 20240310 WA0183

Majalisar Dattawa ta nemi Shugaba Tinubu ya shige gaba domin nema wa kananan hukumomi ‘yanci a wajen jihohi, wanda suka ce hakan zai iya magance matsalar tsaro da ake fama da ita da tururuwar da mutane ke yi zuwa birane da kuma rashin aikin yi. Sanata Abdurrahaman Kawu Sumaila ne ya gabatar da kudurin wanda ya ce akwai bukatar a zauna da gwamnoni da masu ruwa da tsaki domin tattauna yadda za a yi kananan hukumomi su samu ‘yancinsu da suka rasa a baya. Kawu Sumaila ya ce a wannan…

Read More

Kano: Hisbah Ta Hana DJ Maza Yin Wasa A Bukukuwan Mata

IMG 20240517 WA0108

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta haramtawa maza DJs yin wasa a bukukuwan da mata a fadin jihar. Babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana hakan a wani taro da wakilan DJs na jihar. Ya ce matakin ya zama dole domin a hana caku?u wa tsakanin maza da mata a lokutan bukukuwa. Sheikh Daurawa ya bayyana cewa daga yanzu mata ne kawai za a bari su gudanar da taron su na mata. Ya ce, “A matsayinmu na jihar shari’ar Musulunci, ba abin yarda ba ne a ce…

Read More

Hanci Da Rashawa: An Sauya Alkalin Dake Shari’ar Ganduje

images 2024 03 06T195109.222

Babbar Al?alin Jihar Kano, Dije Abdu-Aboki, ta sauya wa tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyyar APC na ?asa, Abdullahi Ganduje sabon al?ali. Tsohon gwamnan dai na fuskantar tuhuma ne tare da wasu mutane bakwai ciki har da matarsa Hajiya Hafsah Ganduje. Kamfanin dillancin labarai na ?asa (NAN), ya ruwaito cewa ragowar wa?anda ake tuhuma sun ha?ar da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash properties Limited, da kuma Safari Textiles Limited. Kafin wannan sauyi dai ana gudanar da shari’ar ne a wata babbar kotu mai lamba 4, ?ar?ashin mai…

Read More

‘Yan Bindiga Na Cigaba Da Daukar Rayuka A Zamfara

IMG 20240421 WA0046

Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane uku tare da sace wasu mutane 130 a kauyen Goran Namaye da ke karamar hukumar Maradun a Jihar Zamfara. Wani mazaunin yankin mai suna Salisu Lawali, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa ‘yan bindigar sun yi wa garin kawanya ne da misalin karfe 1:00 na daren ranar Alhamis. Lawali ya kara da cewa wadanda aka yi garkuwa da su galibi mata ne da kuma wasu maza, inda ya tabbatar da…

Read More

Karbar Alawus Tudu Biyu: Barau Jibrin, Ndume Da Wasu Sanatoci 38 Na Iya Rasa Kujerun Su

IMG 20240517 WA0101

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Sanatoci a?alla 40 ne ka iya rasa kujerar su, saboda kasancewar su mambobi a Majalisar Dattawa da kuma Majalisar ECOWAS ta Afrika ta Yamma, kuma duk suke kar?ar alawus-alawus daga majalisun biyu, abin da ya karya doka. Wasu daga cikin wa?anda tsigewar ka iya shafa sun ha?a Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, wanda a yanzu haka shi ne Kakakin Majalisar ECOWAS na Ri?on, Ali Ndume, Abiodun Olujimi, Smart Adeyemi, Tolu Odebiyi da Mshelia Haruna, da kuma wasu da…

Read More

Gidajen Yada Labarai Za Su Ci Gajiyar Samun Riba Ta Bai Daya Daga Gwamnatin Tarayya

IMG 20240407 WA0063

Shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci ma’aikatar masana’antu da harkokin kasuwanci da bankin kula da masana’antu na ?asa da su fa?a?a shirin samun riba na bai ?aya zuwa ga gidajen ya?a labarai. Ministan ya?a labarai na ?asa Alhaji Muhammad Idris ya sanar da hakan lokacin da ya karbi ba?uncin ?ungiyar gidajen ya?a labarai masu zaman kansu na ?asa a birnin tarayya Abuja. Ministan ya ?ara da cewar shirin cin gajiyar riba ta bai ?ayan wani tsari da gwamnatin tarayya ta fito dashi domin karfafa ayyukan ‘yan kasuwa da kasuwanci a…

Read More

Sauya Takardun Naira: Tsohon Gwamnan Banki Zai Gurfana Gaban Kotu

Hukumar da ke ya?i da masu yi wa arzikin Najeriya ta’annati, EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin ?asar, Godwin Emefiele ranar Laraba bisa bayar da izinin buga sabbin takardun naira na miliyan 684.5 a kan naira biliyan 18.96. Tun farko an tsara gurfanar da shi ne ranar 30 ga watan Afrilu da ya gabata amma aka ?age ranar bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kotun da kuma ?angarorin. A tuhume-tuhumen hu?u da aka shigar a kansa, EFCC ta yi zargin Emefiele ya yi burus da umarnin kotu…

Read More

Matsalolin Najeriya: Jagororin ‘Yan Adawa Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

images (5)

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ?an takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, da takwaransa na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi, sun yi ganawar sirri a Abuja ranar Litinin. Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ne, ya wallafa hotunansa tare da Obi a yayin ganawar a kan X. Obi ya kuma yi wata ganawa ta daban da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido. Obi ya kuma yi wata ganawa ta daban da…

Read More

Kaduna: Da Ni Ne Gwamna, Da El-Rufa’i Ya Gane Shayi Ruwa Ne – Shehu Sani

images (36)

Daga Ibrahim Ammani Tsohon ?an Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya soki lamirin gwamnatin Jihar kan gaza yin wani kata?us akan tsohon gwamnan jihar El Rufai da mu?arrabanshi wa?anda suka talauta jihar da mugun bashi. Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna Sanata Shehu Sani yace abin takaici ne yadda gwamnatin jihar ke shirin cika shekara guda akan mulki amma barayin da suka talauta jihar suna walwala cikin gidajensu ba tare da wata takura ba. “Ina tabbatar muku da ni ne Gwamnan jihar Kaduna…

Read More

Babu Ruwan Tinubu Da Rashin Zaman El-Rufai Minista, Matsalarshi Ce Da ‘Yan Majalisa – Bagudu

IMG 20240316 WA0102

Ministan kasafin ku?in Najeriya, Atiku Bagudu ya bayyana cewa babu ruwan shugaba Bola Tinubu da rashin zaman tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai minista a gwamnatin sa Bagudu ya fa?i haka yayin da yake amsa tambayoyi daga PREMIUM TIMES yayi tattaunawa da ta musamman da ya yi da jaridar a Abuja. Da aka tambaye shi ko me ya sa El-Rufai bai iya samun kujerar minista a gwamnatin Tinubu ba, Bagudu ya ce ” Ai Tinubu ya yi wa El-Rufai riga har da wando domin ya aika da sunansa majalisa a tantance…

Read More

Alaramma Ya Fasa ?wai, Ya Fallasa Yadda Aka Saye Malamai A Zaben 2023

IMG 20240512 WA0041

Alaramma Ismail Maiduguri ya zargi wasu daga cikin malaman musulunci da kiristanci da biyewa ‘yan siyasa lokacin zabe Malamin Al-Kur’anin ya ce yawan cikan sahu a masallatai da coci ake amfani da su a wajen sayen bakin malamai Gwani Ismail Maiduguri ya ce tun da an karbi kudin ‘yan siyasa, dole yanzu ba za a iya kokawa da irin mulkinsu ba Ismail Maiduguri ya tofa albarkacin bakinsa game da halin da Najeriya take ciki a karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu. Alhafiz Ismail Maiduguri ya ce a yanzu ‘yan siyasa sun…

Read More

Ba Za Mu Amince Da Harajin Internet Ba Har Sai An Samar Wa ‘Yan Najeriya Hanyoyin Samu – Sanata Ndume

IMG 20240512 WA0033

Sanata Ali Ndume ya soki harajin yanar gizo da babban bankin Najeriya ya bullo da shi kwanan nan, inda ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya ba za ta iya ci gaba da dorawa ‘yan Najeriya haraji ba tare da kara musu kudaden shiga ba. Dan majalisar Dattawa na jam’iyyar All Progressives Congress mai wakiltar mazabar Borno ta kudu ya bayyana haka a shirin Siyasar Yau na Channels Television a Jiya Juma’a. Ndume ya jaddada cewa harajin da aka saka ta yanar gizo zai kara dora wa ‘yan Najeriya nauyi, Yana mai…

Read More

LASSA: Mutum 857 Sun Kamu Yayin Da Ta Hallaka Mutum 156 A Bana – NCDC

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta bayyana cewa Zazzabin Lassa ta yi ajalin mutum 156 sannan mutum 857 sun kamuwa da ita daga Janairu zuwa ranar 28 ga Afrilu 2024. Hukumar ta ce alkaluman yaduwar cutar ya nuna cewa adadin yawan mutanen da cutar ta kashe a wannan lokaci ya zarce yawan mutanen da cutar ta kashe a irin wannan lokacin shekarar 2023. NCDC ta ce an samu karuwa a yawan mutanen dake kamuwa da cutar daga mutum 11 a mako 16 zuwa mutum 14 a mako 17.…

Read More