Shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu bayan dawowarsa daga godon tafiya ya tarar da wani umarnin Babban Bankin Najeriya na CBN na shirin karawa Yan Najeriya ku?i, kaso 0.5 Sai dai Shugaban Tinubu ya nuna rashin jin dadinsa tuni ya tura umarni akan Babban Bankin Najeriya CBN ya sauka daga kan wannan ku?iri na karawa yan Najeriya haraji a bankuna don samar da tsaron yanar gizo.. Tinubu ya bayyana cewa, wannan tsari na babban Bankin kasa bai da ce da wannan lokacin ba, saboda halin da Yan kasa ke ciki a…
Read MoreAsusun Bada Lamuni Na Duniya (IMF) Ya Soki Lamirin Tinubu Na Dawo Da Tallafin Mai A Boye
Asusun ba da lamuni da duniya (IMF) ya nuna damuwa kan yadda Bola Tinubu ya dawo da tallafin mai a boye. Hukumar ta ce dawo da tallafin da aka yi a boye zai cinye kusan rabin kudin shiga da kasar za ta samu daga arzikin man fetur. Asarar da Najeriya za ta yi IMF ta ce matakin zai la?ume akalla N8.43trn daga cikin N17.7 trn da ake sa ran samu daga cire tallafin man fetur. Wannan na kunshe ne a cikin wani sabon rahoto da hukumar ta fitar kan Najeriya…
Read MoreBabu Gaskiya A Rahoton Asusun Bada Lamuni Na Raguwar Farashin Kayayyaki A Najeriya – Masana
Wasu masana tattalin arziki a Najeriya sun ce hasashen da Asusun Lamuni na Duniya IMF ya yi cewa za a samu raguwar hauhawar farashin kaya a kasar a karshen bana, romon baka ne kawai. Masanan sun ce wannan ba abu ne mai yiwuwa ba matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba. Cikin wata hira da ya yi da BBC, Dakta Murtala Abdullahi Kwara, shugaban sashen nazarin tattalin arziki na jami’ar Umaru Musa ‘Yar-Aduwa da ke Katsina, ya ce ko shakka babu hasashen da ya zo daga masana, to…
Read MoreZamfara: ‘Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Yankin Bilbis
Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewa, Yan ta’adda sun kai mummunan hari a garin Bilbis dake Jihar inda suka kashe mutane kusan 20 da suka kunshi maza da mata da kuma kananan yara. Rahotanni sun ce wadannan ‘yan ta’adda sun kai harin ne a ranar alhamis inda suka kwashe sama da sa’oi 2 suna aika aika tare da jikkata mutane da dama a garin, kuma yanzu haka wasu daga cikin su na asibiti inda suke karbar magani. Shaidun gani da ido sun bayyanawa…
Read MoreKetare: Mahamat Deby Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Chadi
Sakamakon za?en shugaban kasa a Chadi ya bayyana jagoran mulkin Sojin Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin wanda ya lashe zagayen farko na za?en wanda ke nuna yiwuwar ya iya tsawaita wa’adin mulkin iyalan gidan Deby na wasu karin shekaru. Za?en na ranar Litinin ya kawo karshen mulkin ri?on ?warya na shekaru 3 da Chadi ta fuskanta tun bayan mutuwar shugaba Idris Deby Itno a fagen daga wanda ya baiwa ?ansa Janar Mahamat Deby damar jan ragamar kasar mai fama da rikice-rikice baya ga ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda. Sakamakon za?en…
Read MoreMajalisar Dattawa Ta Amince Da Dokar Hukuncin Kisa Ga Dillalan Muggan Kwayoyi
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da ?udurin dokar hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ?wayoyi a fa?in ?asar, bayan ?udurin ya tsallake karatu na uku a zauren majalisar. Majalisar ta amince ta ?udurin bayan kwamitin majalisar kan ayyukan ya?i da fataucin miyagun ?wayyoyi, ?ar?ashin jagorancin Sanata Tahir Munguno ya gabatar da rahotonsa kan sabuwar dokar a zauren majalisar. Yayin da take sake nazarin dokar, majalisar ta amince da dokar hukuncin kisan ne domin ?arfafa ayyukan hukumar ya?i da fataucin miyagun ?wayoyi ta ?asar. A lokacin muhuwar, babban mai tsawatarwa na…
Read MoreBai Kamata Mu Bari ‘Yan Ta’adda Su Gagare Mu Ba – Sarkin Musulmi
Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewa mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhamma Sa’ad Abubakar na uku ya shawarci ‘yan Najeriya da su fahimci ?alubalen da ke gabansu domin tunkarar su. Sultan ?in dai ya fa?i hakan ne yayin wata ziyara da ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru ya kai masa a fadarsa a yau Juma’a. “Bai kamata mu bari wani ya samu galaba a kanmu ba. Ministan tsaro ya san irin girman alhakin da ke rataye a wuyansa. Na kuma yi amannar cewa yana tuntu?ar masu ruwa…
Read MoreMajalisar Wakilai Ta Bukaci A Dakatar Da Shirin Harajin Internet Da Gwamnatin Tarayya Ta Bullo Dashi
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Majalisar Wakilai ta bayar da umarnin dakatar da Babban Bankin na CBN da gaggawar dakatar da aiwatar da harajin ta yanar gizo da babban bankin ya kaddamar, kamar yadda dokar ta tanada. Majalisar ta nuna damuwarta kan yadda ‘yan Najeriya zasu iya fahimtar harajin da babban bankin ya fitar, domin bai yi daidai da ka’idojin da ke kunshe a cikin sashe na 44 (2a) na dokar aikata laifuka ta yanar gizo ba dangane da masu karbar harajin. A martanin…
Read MoreKaduna: Za A Kaddamar Da Shirin Hadakar Makarantu Kan Batun Tsaro
Gwamnatin Jihar Kaduna zata hade wasu makarantun Sakandare dana firamare wajen guda da yawan su ya kai 359 dake yankunan da matsalar tsaro ta fi Kazanta a fadin Jihar. Manufar hakan shi ne tabbatar da cewar ko wane Yaro ya sami damar zuwa makaranta don samin ilimin daya da ce duk da kalubalen tsaro. Gwamnatin Jihar ta dauki wannan matakin ne bayan data sami rahoton raguwar alkaluman adadin Yaran da suke zuwa makaranta, saboda barazanar tsaro. Gwamnan Jihar Sanata Uba Sani ne yake bayyana haka ta bakin Shugaban ma’aikatan Gwamnatin…
Read MoreMajalisar Dattawa Ta Amince Da Dokar Hukuncin Kisa Ga Masu Safarar Kwayoyi
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kudirin dokar da ya bukaci hukuncin kisa kan masu safarar miyagun kwayoyi a kasar. Wannan ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitocin da ke kula da harkokin shari’a, ‘yancin dan Adam, dokar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar. Shugaban kwamitin shari’a da ‘yancin dan adam, Sanata Mohammed Monguno daga jihar Borno ta Arewa, shine ya gabatar da rahoton yayin zaman majalisar na ranar Alhamis. Kudirin dokar wanda ya tsallake karatu na uku, na da nufin sabunta dokar haramta amfani da magunguna masu…
Read MoreBaragurbin Ministoci Ne Suka Sa Ba A Ganin Kokarin Tinubu – Sanata Ibrahim
Yawancin ministocin da shugaban kasa Bola Tinubu ya na?a ba sa kokari a cewar Jimoh Ibrahim, Sanata mai wakiltar Ondo ta Kudu a jam’iyyar APC. Ibrahim ya kuma ce wasu daga cikin ministocin akwai zargin cin hanci da rashawa a tare da su, yayin da wasu Yan Dagaji ne kuma ba sa tabuka komai. Sanatan ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels. A cewar dan majalisar tarayyar, Tinubu yana da tsarin “mafi kyau” da zai tafiyar da mulkin kasar, amma babu wani tsari da mataimaka…
Read MoreBadakalar Biliyan 2.7: Kotu Ta Bada Belin Hadi Sirika Da ‘Yarsa
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, a zamain mulkin Muhammadu Buhari, Hadi Sirika da ‘yarsa Fatima kan naira miliyan 100 kowannen su. A ran Alhamis ne aka gurfanar da Sirika da ?arsa a gaban kotun. Hukumar EFCC ce ta maka tsohon ministan a kotu domin a kwato wasu Naira biliyan 2.7 da take zargin an tafka harkalla a kansu lokacin yana minista. Sirika ya yi shekara takwas ya na Ministan sufuri sannan an gurfanar da shi tare da ‘yarsa Fatima,…
Read MoreSERAP Ta Bukaci Tinubu Ya Yi Amfani Da Karfin Iko Wajen Hana CBN Amfani Da Harajin Internet
Kungiyar Rajin Kare Ha??in Jama’a ta SERAP, ta yi kira ga Shugaban ?asa, Bola Tinubu cewa , “ya yi amfani da ?arfin ikon sa ya gaggauta taka wa Babban Bankin Najeriya (CBN) burki, kada ya bari bankuna su fara cirar Harajin Da?ile Har?allar Ku?a?e ta Hanyar Intanet, wato ‘Cybersecurity’ da aka ?a?aba cikin wannan satin. SERAP ta ce ?a?aba wa ‘yan Najeriya biyan harajin ta hanyar cire masu harajin daga ku?a?en taransifa a bankuna, da Gwamnan CBN Yemi Cardoso zai fara, ya karya Dokar Najeriya ta 1999 da aka yi…
Read More‘Yan Najeriya Miliyan 32 Za Su Fuskanci Matsananciyar Yunwa A Watan Yunin Bana
A cewar rahoton, adadin mutanen da zasu fuskanci matsalar karancin abinci a yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar afirka a wannan dan tsakani zai kai kimanin mutane milyan 52 kwatankwacin kaso 12 cikin 100 na mutanen da aka tantance. Akwai yiyuwar cewar akalla ‘yan Najeriya miliyan 32 ne zasu fuskanci wani yanayi mai kama da matsananciyar yunwa a tsakanin watanin Yuni da Agustar shekarar da muke ciki matukar ba’a dauki matakan gaggawa ba, a cewar rahoton Cadre Harminise’ na baya-bayan nan, wanda kwamitin kai dauki na kasa da kasa da gwamman…
Read MoreDole ‘Yan Najeriya Su Rungumi Sabon Tsarin Harajin Babban Banki – Babban Lauya
Tsohon kakakin dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su sake jikinsu domin rungumar tsarin Lauyan ya bayyana haka ne a ran Laraba 8 ga watan Mayu inda ya ce Tinubu ya na matukar jin tausayin ‘yan kasar Abuja – Daniel Bwala, tsohon kakakin dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ba ‘yan Najeriya shawara. Bwala ya bukaci ‘yan ?asar su yi gaggawar sabawa da tsare-tsaren Shugaba Bola Tinubu musamman kan harajin tsaron yanar gizo. Bwala ya musanta cewa Tinubu bai kula da halin da…
Read MoreMajalisar Wakilai Ta Ki Amincewa Da Kudurin Dakatar Da Sabon Tsarin Harajin Internet
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Majalisar Wakilai ta ?i amincewa da kudirin dakatar da sabon harajin internet da Babban bankin Najeriya ya bu?aci Bankuna Su fara A zaman majalisar na ranar Laraba, Hon. Mansur Manu Soro ya nuna damuwarsa, inda ya nuna cewa shirin karbar harajin bai dace ba, musamman idan aka yi la’akari da kalubalen da ‘yan Najeriya da dama ke fuskanta a halin yanzu. ‘Yan majalisar sun bayyana imanin cewa bai kamata alhakin sarrafa kudaden da aka tara ya kasance ?ar?ashin kulawar…
Read MoreCin Amanar Kasa: Hadi Sirika Da ‘Yarsa Za Su Gurfana Gaban Kotu
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika da ‘yar sa za su gurfana a gaban kotu domin fuskantar tuhuma kan badakalar kwangilar Naira Biliyan 2.7. Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta shirya gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, a gaban mai shari’a Sylvanus Oriji a babbar kotun babban birnin tarayya Abuja, Maitama, a wannan Alhamis mai zuwa. An shirya gurfanar da shi a gaban kotu tare da wasu mutane uku: diyarsa, Fatima; Jalal Hamma; da kuma Al-Duraq Investment Ltd, bisa zargin yin amfani da…
Read MoreZa Mu Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zanga Muddin Ba A Janye Sabon Tsarin Harajin Internet Ba – Kungiyar Kwadago
Kungiyar ?wadago ta TUC a Najeriya ta yi barazanar gudanar da gagarumar zanga-zanga tare da dakatar da al’umura a fa?in ?asar matu?ar gwamnatin tarayya ba ta soke sabon harajin tsaron intanet da Babban bankin ?asar ya ?ullo da shi ba. ?ungiyar ta yi barazanar ce a wata sanarwa da ta fitar yau Laraba, wadda ta samu sa hannun shugaban ?ungiyar, Festus Osifo. Hakan na zuwa ne bayan ita ma ?ungiyar ?wadago ta TUC ta soki lamirin sabon harajin, wanda ta bayyana a matsayin wani gagarumin nauyi da gwamnati ke ?ora…
Read MoreECOWAS Za Ta Kafa Dakaru Na Musamman Domin Yakar Ta’addanci A Yammacin Afirka
Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka Ecowas ta ce za ta kafa dakarun ko-ta-kwana domin tunkarar matsalar ‘yan ta’adda masu i?irarin jihadi da ke tayar da zaune tsaye a ?asashe daban-daban, kamar yadda shafin intanet na The Nation mai zaman kansa a Najeriya ya rawaito. Kwamishinan Ecowas Abdel-Fatau Musah ya fadi hakan ne jiya a Abuja cewa ?ungiyar na bukatar tara dala biliyan 2.4 ga dakarun, inda ?asashe mambobin kungiyar suka bayar da rabin adadin. “A yau, Burkina Faso ta zarce Afganistan a matsayin kasa mafi fama da ta’addanci a…
Read MoreSanatocin Arewa Sun Soki Jan Kafar Da Ake Yi Wa Aikin Hanyar Kano Zuwa Maiduguri
Saanatocin arewacin Najeriya sun nemi gwamnatin Najeriya ta farfado da aikin hanyar da ta tashi daga birnin Kano zuwa Maiduguri na jihar Bornon wanda aka bayar da kwangilar aikinsa tun lokacin mulkin tsohon shugaban ?asar Olusegun Obasanjo. Sanata mai wakiltar maza?ar Kano ta Kudu, Abdurrahaman Kawu Sumaila ne ya gabatar da kudurin wanda ya nemi a mayar da hankali kan titin da ya tashi daga Gaya zuwa Wudil. A lokacin da ya bayar da tasa gudumawar, Sanata Muhammad Danjuma daga jihar Gombe ya nemi a mayar da hankali wajen kammala…
Read More



