Shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci ma’aikatar masana’antu da harkokin kasuwanci da bankin kula da masana’antu na ?asa da su fa?a?a shirin samun riba na bai ?aya zuwa ga gidajen ya?a labarai.
Ministan ya?a labarai na ?asa Alhaji Muhammad Idris ya sanar da hakan lokacin da ya karbi ba?uncin ?ungiyar gidajen ya?a labarai masu zaman kansu na ?asa a birnin tarayya Abuja.
Ministan ya ?ara da cewar shirin cin gajiyar riba ta bai ?ayan wani tsari da gwamnatin tarayya ta fito dashi domin karfafa ayyukan ‘yan kasuwa da kasuwanci a fadin tarayyar Nijeriya.
“Ina tabbatar muku ma’aikatar kula da harkokin yada labarai da ni a karan kaina muna tare da gidajen ya?a labarai ?ari bisa ?ari wajen bayar da dukkanin gudummawar da ta kamata”.
Daga nan Ministan ya bukaci ‘ya’yan ?ungiyar gidajen ya?a labaran da su bayar da dukkanin taimako da gudummuwar da ta kamata wajen ciyar da Najeriya gaba.
Tun farko da yake jawabi shugaban kungiyar gidajen ya?a labaran Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan ya bayyana wasu matsaloli da gidajen ya?a labarai masu zaman kansu suke fama dasu a ?asa, inda ya jaddada bukatar ?ungiyar na ganin gwamnati ta shigo cikin lamarin ?ungiyar domin kai wa ga cimma nasara.
