Babu Ruwan Tinubu Da Rashin Zaman El-Rufai Minista, Matsalarshi Ce Da ‘Yan Majalisa – Bagudu

IMG 20240316 WA0102

Ministan kasafin ku?in Najeriya, Atiku Bagudu ya bayyana cewa babu ruwan shugaba Bola Tinubu da rashin zaman tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai minista a gwamnatin sa

Bagudu ya fa?i haka yayin da yake amsa tambayoyi daga PREMIUM TIMES yayi tattaunawa da ta musamman da ya yi da jaridar a Abuja.

Da aka tambaye shi ko me ya sa El-Rufai bai iya samun kujerar minista a gwamnatin Tinubu ba, Bagudu ya ce ” Ai Tinubu ya yi wa El-Rufai riga har da wando domin ya aika da sunansa majalisa a tantance shi ya zama minista amma daga ?arshe abin ya gagara.

” Mutumin da ya ke son ka shine zai bukaci ya yi maka irin haka kuma ya yi abinda ya dace tunda har ya aika da sunansa a tantance shi.

” Majalisa ce ba ta amince da shi ba, kun ga babu ruwan Tinubu a ciki. babu abinda shugaban kasa zai iya yi kan haka saboda shi ya yi abinda doka ta ce ya yi, majalisa ce ta yi aikinta.

Sai dai kuma duk da haka akwai da yawa cikin msu sharhin siyasa a Najeriya da suke cewa akwai yiwuwar fadar gwamnatin tarayya ba ta son El-Rufai ya shiga cikin gwamnatin.

Suna ganin kamar ita kanta gwamnatin na tsoron El-Rufai saboda hazakar sa da kuma kaifin basira da hangen nesa, kada wara rana ya kwanto wa gwamnatin kurar da ba a iya ?aurewa.

Related posts

Leave a Comment