Matsalolin Najeriya: Jagororin ‘Yan Adawa Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

images (5)

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ?an takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, da takwaransa na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi, sun yi ganawar sirri a Abuja ranar Litinin.

Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ne, ya wallafa hotunansa tare da Obi a yayin ganawar a kan X.

Obi ya kuma yi wata ganawa ta daban da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.

Obi ya kuma yi wata ganawa ta daban da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.

A cikin wata sanarwa bayan tarurrukan, mai magana da yawun yakin neman zaben shugaban kasa na LP, Tanko Yunusa, ya ce Mista Obi ya ziyarci Messrs Abubakar (Atiku), Saraki da Lamido don tattaunawa kan “yanayin kasa”.

“Dangane da halin da al’ummar kasar ke ciki da kuma karuwar rashin tabbas na rayuwar talakawa da marasa galihu, Obi a ranar Litinin ya ziyarci wasu jiga-jigan ‘yan Najeriya, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma ?an takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a za?en 2023, Atiku Abubakar, tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.

Bayan haka Obi ya tattauna matsalolin rashin zaman lafiya, ta’addanci da garkuwa da mutane da suka addabi ?an Najeriya musamman yankin Arewa.

Wannan shine ziyarar farko da Obi na LP ya kaiwa jigajigan PDP tun bayan za?en 2023.

Related posts

Leave a Comment