Shugaban jam’iyyar SDP na Najeriya, Shehu Gabam ya zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da ta gabata da rashin magance matsalolin Najeriya, lamarin da ya ce ya haifar wa gwamnati mai ci fusknatar tarin matsalolin tattalin arziki.
Yayin wata hira a shirin ‘Politics Today’ na gidan Talbijin na Channels, Gabam ya zargi gwamnatin Buhari da gazawa wajen magance matsalolin ?asar.
”Na sha fa?a a lokuta da dama cewa gwamnatin Buhari ita ce gwamnati mafi munin gwamnati da aka ta?a gani na tarihin Najeriya, mulkinsa ne ya gadar wa gwamnatin Bola Tinubu matsin tattalin arzikin da take fuskanta a yanzu”, in ji Gabam.
Shugaban na SDP ya kuma ce gwamnatin Tinubu ta yi gaggawa wajen kawo wasu sauye-sauyen tattalin arziki a ?asar.
“Mun sani ya gaji matsalar tattalin arziki, ha??insa ne ya lalubo hanyoyin farfa?o da shi, amma bai kamata hanyoyi su zama masu tsauri ba, saboda ba za ka iya farfa?o da shi a rana guda ba”, in Gabam.
Tun bayan hawansa mulki, shugaba Tinubu ya ?auki matakai da dama wajen farfa?o da tattalin arzikin ?asar, ciki har da cire talklafin man fetur da ya yi a jawabinsa na farko bayan shan rantsuwa, lamarin da masana ?e ala?antawa da ?ara jefa ?asar cikin matsin rayuwa da ?aruwar hauhawar farashin kayayyaki.
Ko a watan Afrilu ma hukumar ?ididdiga ta ?asar ta ce hauhawar farashi ya kai kashi 33
