Wasu daga cikin wa?anda tsigewar ka iya shafa sun ha?a Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, wanda a yanzu haka shi ne Kakakin Majalisar ECOWAS na Ri?on, Ali Ndume, Abiodun Olujimi, Smart Adeyemi, Tolu Odebiyi da Mshelia Haruna, da kuma wasu da dama.
Lamarin ya taso ne daga wata ?ara da Kungiyar Bin Diddigin ‘Yan Majalisa (ALDRAP) ta shigar a gaban Babbar Kotun Najeriya, Abuja, inda ?ungiyar ya maka ‘yan majalisar kotu.
ALDRAP dai tun kafin ta je kotu, sai da ta fara yin kira ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio cewa ya ayyana kujerun sanatocin cewa ba su ne a kai ba, an tsige su, saboda sun shiga wata majalisa sun ha?a mamba ?in majalisa biyu, wato ta Najeriya da ta ECOWAS, kuma duk ana biyan su a majalisun biyu.
Yayin da suka ga Akpabio bai yi komai ba, sai ALDRAP ta aika masa da takardar garga?i, cewa za su ?auki matakin shari’a.
A cikin wasi?ar da suka aika a ranar 8 ga Afrilu, mai ?auke da sa hannun Sakataren ALDRAP, Tonye Clinton Jaja, ?ungiyar ta yi garga?in cewa, “Idan Majalisa ba ta ?auki mataki a cikin kwanaki bakwai ba, to za ta garzaya kotu.
Sun jaddada cewa dokar Najeriya Sashe na 68(1) na Kundin Dokokin 1999, ya haramta wa sanata ya zama mamba na Majalisar ECOWAS. Kuma ita ma Dokar 2017 ta ECOWAS ta Sashe na 18 ya yi hani da zama mamba a majalisa biyu.
Sun ce ita ma ECOWAS ta haramta ?an majalisa ya zama mamba a wuri biyu, kamar yadda ta haramta masa kar?ar alawus-alawus a majalisa biyu.
ALDRAP ta ro?i Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta jaddada dokar shiga Majalisar ECOWAS, wato inda doka ta ce, duk mai sha’awar zama mamba a Majalisar ECOWAS ko ta Afirka, to tilas sai ya fara yin murabus, ya sauka daga kujerar sa a Majalisar Dattawa.
Sun kuma ro?i kotu ta dakatar da biyan sanatocin su 40 dukkan albashin su da alawus-alawus ?in da Majalisar Dattawa ke biyan su, saboda kwanan nan aka ?addamar da su mambobin ECOWAS, wasu kuma mambobin Majalisar Afrika.”
ALDRAP ta kuma ro?i kotu ta bai wa INEC umarnin shirya za?ukan cike-gurbi a yankunan sanatocin su 40, domin a za?i wa?anda za su maye gurbin su a Majalisar Dattawa, a cikin kwanaki 30.
A ranar 4 ga Afrilu ne Shugaban ?asa Bola Tinubu ya ?addamar da Majalisar ECOWAS ta Shida, bayan cikar wa’adin ta Biyar a ranar 8 ga Maris, 2024.
