Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Sace Malamai A Jami’ar Dutsinma

IMG 20240211 WA0197

Wasu ?anbindiga sun sace wasu malaman jami’ar tarayya ta Dutsin Ma da ke jihar Katsina, Farfesa Richard Kyaram da kuma Dakta Hamza daya.

An tattaro cewa an sace Mista Kyaram ne tare da dansa, Solomon.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a GRA Dustin Ma da misalin karfe 1:am na jiya Litinin.

An kuma tattaro cewa ?an ta’addan sun mamaye al’umma da nagartattun makamai inda suka rika harbe-harbe.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ?ansandan jihar Katsina, Abubakar Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce rundunar ta na aiki tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro domin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

Related posts

Leave a Comment