Shugaban jam’iyyar, NNPP, a jihar Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa ya ce masu zagon kasa ba za su iya dakatar da makomar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, Rabiu Kwankwaso ba.
Dungurawa ya ce wadanda ke yakar Kwankwaso ne bayan rahotannin da ke cewa Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC na binciken sa.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa na binciken Kwankwaso kan badakalar Naira biliyan 2.5.
Sai dai da yake jawabi ga manema labarai a Kano, jigon na NNPP ya bayyana rahotannin a matsayin karya, yana mai jaddada cewa Kwankwaso mutum ne mai gaskiya da iya aiki.
Ya ce: “Mun sha ganin irin wannan jita-jita a lokuta daban-daban.
“Bari su ci gaba da jita-jita. Ko sun so ko ba sa so, Kwankwaso ya kasance mutum daya tilo mai mutunci, mutuntawa, farin jini, da iya mulkin kasar nan.
“Wannan jita-jita ta fito ne daga makiya, jahilci ya raba su, kuma wawa ya yarda da shi. Mun godewa Allah da ba mu duka ukun ba ne. Mu masoyansa ne, ba mu jahilci aikinsa ba, kuma ba wawaye ba ne.
“Duk wadannan ba za su hana kaddarar sa ba. Amma ya kamata su tuna cewa jita-jita ba ta ?arawa wani daraja; maimakon haka, za su haifar masa da farin jini.”
