Keyamo ya bayyana haka a Abuja, a taron Majalisar Zartaswa ta ?asa.
“Za mu sake ko sabunta kwangilar jinginar da filayen jiragen biyu, domin a fito da komai a yi komai ke?e-da-?e?e.
Ya ce har yanzu haka an dakatar da batun kafa Nigerian Air.
Ya ?ara da cewa Jirgin Kamfanin Ethiopian Airlines ne tsohon Ministan Hadi Sirika ya shafa wa fenti da tutar Najeriya, ya ?addamar da shi.
“Tilas Nigerian Air ya zama na cikin gida kacokan”, inji Keyamo.
Cikin shekarar da ta gabata ne tsohon Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya yi gidogar ?addamar da Nigerian Air, Kwanaki biyu kafin ya sauka daga minista.
Kwanan nan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin sa da na ‘yar sa, bayan an dam?e shi ana neman Naira biliyan kusan 20 a hannun sa.
