Karancin Albashi: Kungiyar Kwadago Ta Cimma Yarjejeniya Da Gwamnatin Tarayya

FB IMG 1709098029346~2

Rahotanni sun nunar da cewa, an cimma wannan matsayar yayin wani taro da kungiyar ta yi da kwamitin kasa kan mafi karancin albashin da aka fara da misalin karfe biyar na Yammacin Litinin din da ta gabata zuwa wajejen karfe 11 na dare.

A cewar sakataren gwamnatin Tarayyar Najeriyar George Akume kwamitin, zai rinka ganawa a kowacce rana tsawon mako guda domin lalubo bakin zaren warfare takaddamar da ke tsakanin gwamnatin da wakilan ma’aikatan.

Hadakar kungiyoyin kodogon da gwamnatin Tarayyar dai, sun sanya hannu kan wata yarjejeniya da suka cimma.

Koda yake ba a kai ga fitar da cikakkun bayanai kan yarjejeniyar ba, amma jaridaru sun ruwaito cewa, gwamantin Najeriyar ta amince da biyan sama da Naira dubu 60 a matsayin mafi karancin albashin.

Haka kuma, babu wani ma’aikaci da zai fuskanci hukunci sakamakon yajin aikin gama-garin da kungiyar kodogon Najeriyar NLC ta kaddamar a jiya Litinin, wanda ya kassara komai a kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka.

Related posts

Leave a Comment