?an takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi, ya bi sahun dandazon magoya bayan jam’iyyar, inda ya ziyarci shagabannin jam’iyyar a helkwatar su da ke Abuja.
Shugaban jam’iyyar na kasa wanda ya kaddamar da sabbin ‘yan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar a karkashin jagorancin Barista Julius Abure, ya bukaci ‘yan kwamitin su sanya rayuwar ‘yan Nijeriya da ma kasa baki daya a sahun farko na dukkan al’amurran su.
Peter Obi, ya ce ya kasance a sakatariyar jam’iyyar ne musamman don ya ziyarci shugaban ta, ya na mai shan alwashin ci-gaba da yin duk mai yiwuwa don ganin an sasanta matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta a cikin gida.
Ya ce duk kalubalen da Nijeriya ke fuskanta su na da nasaba ne da rashin inganta rayuwar al’umma, musamman bangaren samar da abinci da tsaro da ilimi da kiwon lafiya da kuma ruwan sha.
Peter Obi ya kara da cewa, yanzu abin da ya rage kawai shi ne tunanin yadda rayuwa za ta iya dorewa kafin wani lokaci, domin babu abin da ya damu ‘yan siyasa illa tunanin zabe na gaba ba zancen rayuwar al’umma ba, amma shi a wurin sa, idan jama’a su ka rayu zuwa lokacin zabe sai a yi maganar da ta shafi hakan.
Ya ce abu mai mahimmanci shi ne, fuskantar inda Nijeriya ta dosa tare da tabbatar da cewa ta na murmurawa, to a nan ne jam’iyyar Labour za ta iya tagazawa.
A na sa jawabin, shugaban jam’iyyar Labour na kasa Julius Abure, ya ce kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa ya ji dadin ziyarar da dan takarar shugaban kasar da magoya bayan ta su ka kai masu.
Ya ce lokaci ya yi da bangarorin da ba su jituwa da juna sanadiyyar babban taron Nnewi za su hada kai domin tabbatar da samun nasarar jam’iyyar a zabe na gaba.
Julius Abure, ya ce taron dai ya riga ya wuce, don haka duk wadanda ke rike da juna a zuciya ana rokon su maida wukar su kube, su hada kai tare da ba su goyon baya a gina jam’iyyar a samar da kyakkyawar Nijeriya.
Ya ce ya na da yakinin cewa, matukar aka kai zuciya nesa tare da tunkarar abin da ya shafi ci-gaban Nijeriya haka za ta cimma ruwa.
Shugaban jam’iyyar Labour na birnin tarayya Abuja Peter Dugwu da ya shiraya ziyarar, ya ce reshen jam’iyyar na birnin tarayya ya na hada hannu da kwamitin gudanarwar jam’iyyar domin tabbatar da ganin an yi nasara a zabubbukan kananan hukumomi.
Sa hannun:
OBIORA IFOH
Sakataren Yada Labarai Na Jam’iyyar Labour
