Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewa mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhamma Sa’ad Abubakar na uku ya shawarci ‘yan Najeriya da su fahimci ?alubalen da ke gabansu domin tunkarar su.
Sultan ?in dai ya fa?i hakan ne yayin wata ziyara da ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru ya kai masa a fadarsa a yau Juma’a.
“Bai kamata mu bari wani ya samu galaba a kanmu ba. Ministan tsaro ya san irin girman alhakin da ke rataye a wuyansa. Na kuma yi amannar cewa yana tuntu?ar masu ruwa da tsaki domin su taimaka masa . Muna aiki tare kuma ba za mu daina ba.
Sarkin na Musulmi ya jaddada cewa sarakan gargajiya za su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya ya ?ore a ?asar.
To sai dai Sultan ?in ya nemi goyon bayan al’umma ga jami’an tsaron Najeriya wa?anda ya ce suna jefa rayuwarsu cikin ha?ari saboda kare ?asa.
