Labarin dake shigo mana yanzu daga Jihar Kaduna na bayyana cewar rundunar ‘Yan sandan Jihar sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga biyu da suka addabi yankin ?aramar Hukumar Giwa yayin wata arangama.
Dakarun rundunar 47 Zariya ne suka gamu da ‘yan fashin yayin da suke kan aikin sintiri a kusa da ?auyen Riheyi na garin Fatika ranar Litinin da dare, in ji kakakin rundunar a Kaduna Mohammed Jalige
Da yake magana da Channels TV, Mista Jalige ya ce nan take suka fara fafatawa, inda jami’ansu suka yi nasarar kashe biyu daga cikinsu.
Ya ?ara da cewa ‘yan sanda sun ?wace bindiagar AK-47 da kuma harsasai daga hannun ‘yan fashin.
A ranar Litinin ?in da dare wasu ‘yan fashi suka tare babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya, inda rahotanni suka ce an kashe mutum ?aya tare da sace wasu da dama.
