Saanatocin arewacin Najeriya sun nemi gwamnatin Najeriya ta farfado da aikin hanyar da ta tashi daga birnin Kano zuwa Maiduguri na jihar Bornon wanda aka bayar da kwangilar aikinsa tun lokacin mulkin tsohon shugaban ?asar Olusegun Obasanjo.
Sanata mai wakiltar maza?ar Kano ta Kudu, Abdurrahaman Kawu Sumaila ne ya gabatar da kudurin wanda ya nemi a mayar da hankali kan titin da ya tashi daga Gaya zuwa Wudil.
A lokacin da ya bayar da tasa gudumawar, Sanata Muhammad Danjuma daga jihar Gombe ya nemi a mayar da hankali wajen kammala hanyar musamman ?angaren da ya tashi daga Benishek zuwa Maiduguri wanda ya ce kusan kullum sai an rasa rayuka a kan titin.
Sanata Kaka lawan da yake wakiltar Borno ta tsakiya ya ce da rana ido na ganin ido ana iya yin fashi a kan wannan hanyar ta Benishek zuwa maiduguri, shi ya sa ya nemi majalisa ta matsa ?aimi wajen ganin an kammala aikin.
Ya ce ita kadai ce hanyar da ta hada arewa maso gabashin Najeriya da yankuna masu yawa, ta kuma ratsa jihohin Bauchi kano Jigawa Yobe da kuma Borno.
Mataimakin shugaban Majalisar dattijai, Sanata Barau Jibrin ya goyi bayan wannan kuduri yana cewa “ya kamata a sake duba kwangilar da aka bayar”.
Babbar hanyar wadda ta tashi daga Kano zuwa Maiduguri na daga cikin manyan ayyukan gwamnatin tarayyar Najeriya da ake ganin sun da?e ana jan ?afa wajen kammala su.
