Ketare: Mahamat Deby Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Chadi

IMG 20240511 WA0042

Sakamakon za?en shugaban kasa a Chadi ya bayyana jagoran mulkin Sojin Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin wanda ya lashe zagayen farko na za?en wanda ke nuna yiwuwar ya iya tsawaita wa’adin mulkin iyalan gidan Deby na wasu karin shekaru.

Za?en na ranar Litinin ya kawo karshen mulkin ri?on ?warya na shekaru 3 da Chadi ta fuskanta tun bayan mutuwar shugaba Idris Deby Itno a fagen daga wanda ya baiwa ?ansa Janar Mahamat Deby damar jan ragamar kasar mai fama da rikice-rikice baya ga ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Sakamakon za?en da hukumar za?e ta ANGE ta fitar ya nuna yadda Mahamat Deby da aka fi sani da Kaka ya lashe jumullar kashi 61.3 na yawan ?uri’un da aka ka?a yayinda Firaministan ?asar Success Masra ya lashe kashi 18.53.

Kowanne lokaci daga yanzu ne ake dakon kotun kundin tsarin mulki ta tabbatar da sahihancin za?en.

Sai dai tuni Firaminista Masra ya ?alubalanci sakamakon wanda ya bayyana da marar inganci.

A bangare guda tuni Shugaba Mahamat Deby Itno ya gabatar da jawabin kai tsaye ta gidan talabijin tare da godewa al’ummar ?asar kan za?ensa baya ga shan alwashin samar da yanayi mai inganci ga al’umma.

Tun gabanin sanar da sakamakon za?en anga yadda dubunnan magoya bayan Deby suka fara murnar samun nasara a kan titunan birnin N’Djamena fadar gwamnatin Chadi.

Related posts

Leave a Comment