Za Mu Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zanga Muddin Ba A Janye Sabon Tsarin Harajin Internet Ba – Kungiyar Kwadago

IMG 20240229 WA0092

Kungiyar ?wadago ta TUC a Najeriya ta yi barazanar gudanar da gagarumar zanga-zanga tare da dakatar da al’umura a fa?in ?asar matu?ar gwamnatin tarayya ba ta soke sabon harajin tsaron intanet da Babban bankin ?asar ya ?ullo da shi ba.

?ungiyar ta yi barazanar ce a wata sanarwa da ta fitar yau Laraba, wadda ta samu sa hannun shugaban ?ungiyar, Festus Osifo.

Hakan na zuwa ne bayan ita ma ?ungiyar ?wadago ta TUC ta soki lamirin sabon harajin, wanda ta bayyana a matsayin wani gagarumin nauyi da gwamnati ke ?ora wa talaka.

A ranar Talata ne Babban Bankin Najeriya ya fitar da wata sanarwa wadda ke neman a cire harajin kashi 0.5 cikin ?ari kan duk wata hada-hadar tura ku?i da mutanen ?asar suka yi ta intanet.

Sanarwar TUC ta ci gaba da cewa “babu dabara wajen fito da irin wannan haraji daidai lokacin da ?an Najeriya ke fama da tsadar rayuwa sanadiyyar fa?uwar darajar naira da ?arin farashin man fetur da na lantarki.

Related posts

Leave a Comment