Muna Goyon Bayan ACF Na Hana ‘Yan Arewa Shiga Jihohin Inyamurai – Matasan Arewa

Kungiyar cigaban Matasan Arewacin Najeriya ta nuna goyon bayanta dangane da kiran da kungiyar Dattawan Arewa ta ACF ta yi na hani ga ‘yan Arewa shiga Jihohin Inyamurai sakamakon matsalar tsaro.

?aya daga cikin shugabannin kungiyar Alhaji Imrana Nass ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Kaduna.

Imrana Nass ya ce ai tun asali ya kamata ace Dattawan sun yi wannan kiran ba a yanzu ba, domin halin da ‘yan Arewa ke ciki yanzu a Kudancin Najeriya abin tsoro da tashin hankali ne.

Shugaban Matasan na Arewa wanda ya koka akan kisan gillar da tsagerun Inyamurai suka yi wa Tsohon Hadimin Jonathan Dr. Ahmad Gulak a jihar Imo, yace wannan ba abu bane da za’a lamunta, kuma ya zama wajibi a kafa kwamitin bincike akai.

Dangane da maganar da shugaban kasa Buhari ya yi na cewar tura takai bango ba zai amince da kisan jama’a babu dalili ba, Imrana Nass yace sun zuba ido domin ganin matakin da shugaban zai dauka akai.

Daga karshe Shugaban Matasan ya yi kira ga jama’ar Arewa da su mike domin kare dukiya da rayukan su daga mamayar ‘yan ta’adda kasancewar gwamnati ta nuna gazawarta a fili.

Related posts

Leave a Comment