An Kafa Kwamitin Bincikar Jiragen Sojin Najeriya

Babban hafsan sojan sama na Najeriya (CAS), Air Marshal Oladayo Amao ya kafa wani kwamiti na musamman da ya ?unshi har da manyan tsoffin sojojin da suka yi ritaya don gudanar da binciken lafiyar jiragen soji na ?asar da kuma ?angaren masu kula da su.

Sanarwar da kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar a ranar Talata ta ce aikin kwamitin ya shafi binciken rahoton lafiyar jiragen sojin da ayyukan injiniyanci tare da ba da shawarar matakan inganta ayyuka da amincinsu.

“Kwamitin ?ar?ashin jagorancin Air Vice Marshal Abraham Adole, mataimakin kwamandan ayyukan rundunar Hadin Kai an ba shi wa’adin ya gabatar da rahotonsa kafin 18 ga watan Yunin 2021,” in ji sanarwar.

Related posts

Leave a Comment