Filato: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda

Rahotanni daga Jos babban birnin Jihar Filato na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga ?auke da muggan makamai sun bindige wani mataimakin Kwamishinan ‘yan Sanda har lahira da tsakiyar ranar yau Laraba.

‘Yan Bindigar sun kashe Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda na kasa mai ritaya AIG Christopher Dega a birnin Jos na Jihar Filato da sanyin safiyar yau.

‘Yan bindigar sun dinga zazzaga masa albarusai ne a kirji har sai da ya ce ga garin ku nan.

Wannan dai shine karo na hudu a jere da ‘yan bindiga suke kashe manyan mutane a cikin satin nan.

Related posts

Leave a Comment