An Na?a Kingibe Jakadan Tafkin Chadi

Shugaba Muhammadu Buhari ya na?a Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babagana Kingibe mu?amin Jakada na Musamman a Chadi da Yankin Tafkin Chadi.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.

“An na?a wannan mu?amin ne biyon bayan ?udirorin da aka cimma a taron Kasashen Yankin Tafkin Chadi kan Makomar Kasar Chadi, wanda aka gudanar a ranar 25 Ga Mayu.

“Aikin Jakada na Musamman a Chadi da Tafkin Chadi, shi ne kula da lamurran da ke faruwa a Chadi da Yankin Tafkin Chadi.

“Kuma zai sa ido da kula da kuma sasantawa da ganin an maida ?asar Chadi bisa turbar tsarin dimokra?iyya, a ?arshen wa’adin wannan gwamnatin ri?on-?warya ta sojojin Chadi.

“Zai ri?a aiki kafa?a-da-kafa?a da sauran ?asashen ?ungiyar yankin Tafkin Chadi domin dawo da bun?asar yankin, wanzar da zaman lafiya da kuma inganta tsaro.” Inji sanarwar wadda Boss Mustapha ya fitar, a ranar Litinin a Abuja.

Ya ?ara da cewa Shugaba Buhari ya ?ora wa Kingibe wa?annan ayyuka bisa ya?inin cewa zai yi habbosa wajen ganin ya yi amfani da wannan dama domin a samu wanzuwar dawwamammen zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

Related posts

Leave a Comment