Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sako daliban jami’ar Greenfield bayan sama da wata guda a hannunsu cikin dokar daji.
A rahoton gidan talabijin na Channels ya bayyana cewar dalibai 14 aka sake ranar Asabar din nan da muke ciki.
Shugaban kungiyar iyayen daliban, Markus Zarmai da wasu sun je tarban daliban inda ‘yan bindigan sukayi alkawarin ajiyesu.
An tuntubi Kakakin Rundunar yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, kuma ya tabbatar da wannan labari. A cewarsa, har yanzu yana neman bayani amma lallai akwai magana an saki wasu cikin daliban.
“Akwai wannan maganar cewa an saki wasu cikin daliban,” Jalige ya bayyanawa wakilinmu. Wannan ya biyo bayan maganar Sheikh Ahmad Gumi inda yace yan bindigan sun fasa kashesu kamar yadda sukayi barazana.
Idan ba a manta ba a ranar 20 ga watan Afrilu ‘yan bindiga suka kai hari jami’ar dake hanyar Kaduna-Abuja kuma suka hallaka mai gadi, sannan suka arce da daliban dokar daji.
Sun bukaci kudin fansan Naira Miliyan N800, amma da aka ki biyansu bayan kwanki uku, suka kashe dalibai 5 cikin 22 da suka sace.
An tsinci gawawwakin daliban a cikin daji. A hirar da VOA Hausa tayi da shugaban ‘yan bindigan mai suna Sani Idris Jalingo (Baleri), ya ce sun kashe dalibai biyar ne don nunawa duniya cewa gwamnati ta gaza.
A ranar 3 ga watan Mayu, ‘yan bindigan sun yi barazanar kashe sauran dalibai 17 dake hannunsu idan gwamnatin Kaduna bata biya kudin fansa ba.
