Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, yace matu?ar ba’a magance talauci da rashin adalci a Nijeriya ba, to babu wani makami da zai yi nasara a ya?in da ake da rashin tsaro a ?asar nan.
Okorocha, wanda ya yi jawabi a wajen taron shekara-shekara na 2021 NBA, mai taken “Rawar da mutane zasu iya takawa a gwamnatin Najeriya’, yace akwai dangantaka tsakanin talauci da rashin adalci.
Sanatan ya kuma yi fatan Nijeriya za ta cigaba da kasance wa tsintsiya ?aya duk kuwa da kiraye-kirayen a raba ?asar da wasu ke yi daga sassa daban-daban, kamar yadda Daiily Trust ta ruwaito.
Okorocha yace: “Bai kamata mu cigaba da tunanin cewa Nijeriya za ta tarwatse ba, Najeriya babbar ?asa ce kuma ba zata tarwatse ba, bada jimawa ba za’a haifi sabuwar Najeriya.”
“Akwai talauci da rashin adalci a cikin Najeriya, kuma wa?annan abubuwa biyu sun da dangantaka da juna.”
“Matukar ba’a magance rashin adalci da talauci ba, to ko da zaku siyo dukkan makaman duniya domin ya?ar matsalar tsaro, bana ganin za’a samu sakamako mai kyau.”
A wani labarin kuma Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru Ya ?ara Jefa Mu Cikin Matsaloli, inji Shugaba Buhari
Shugaba Buhari yace mutuwar shugaban rundunar Soji da sauran jami’ai 10 ya ?aro matsaloli a ?asar nan, kamar yadda the cable ta ruwaito.
Shugaban yace Allah ne ka?ai yasan da faruwar wannan lamarin, amma ya faru a lokacin da ?asar ke cikin ?alubalen tsaro.
