Rahotannin daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar Hukumar Rarraba Wutar Lantarki ta Abuja, AEDC, ta gutsure wutar lantarkin gidan gwamnatin jihar Niger, wutar majalisar jihar da ta babban asibitin Minna da sauransu kan tarin bashin da ake bin su. Sauran manyan wuraren da ake yankewa wutar sun hada da asibitin kwararru na IBB, gidan ruwa na jihar da sakateriyar jihar. Wannan shi ne karo na uku da aka yankewa gidan gwamnatin jihar wutar lantarki a wannan shekarar sakamakon yadda suka kasa mutunta yarjejeniyar dake tsakaninsu tun a…
Read MoreCategory: Tattalin Arziki
Tattalin Arziki
Tallafin Fetur Ba Zai Tabbata Ba – Shugaban Kasa
Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya sake nanata aniyarsa ta janye tallafin man fetur a 2023, yana mai cewa “ba abu ne mai ?orewa ba idan aka yi la’akari da abin da ke faruwa”. Buhari ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da kasafin ku?in 2023 na naira tiriliyan 20.51 ga gamayyar taron ‘yan majalisar tarayya a ranar Juma’a. A cewarsa: “Maganar tallafin mai abu ne mai cike da cecekuce a ?asarmu tun daga shekaraun 1980. “Sai dai, halin da ake ciki a yanzu ya nuna cewa ba abu ne…
Read MoreKishin Kasa: Buhari Zai Karrama Tsohuwar Ministar Kudi
Shugaban ?asa Muhammadu Buhari zai karrama Shugabar ?ungiyar Cinikayya ta Duniya, Ngozi Okonjo-Iweala da lambar girmamawa ta GCON. Okonjo-Iweala wadda tsohuwar ministar ku?i ce a Najeriya, ta taya ‘yan ?asar murnar cika shekara 62 da samun ‘yancin-kai, inda ta yi amfani da damar wajen gode wa Buhari da ‘yan ?asar. “Ina godiya ga Mai Girma Shugaban ?asa da ‘yan Najeriya saboda girmama ni da za a yi da lambar GCON,” a cewarta cikin wani sa?on Twitter da ta wallafa a yau Asabar. GCON na nufin Grand Commander of the Order…
Read Moree-Naira Karkashin Bizi Mobile, Kama, FMB Ya Samu Karbuwa A Borno
A ci gaban su na samarwa da Matasan Jihar Borno ayyukan yi, Gwamnatin Jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Zulum, da hadin gwiwar kamfanin hada hadar kudi irin na zama ni, wato Bizi Mobile Cashless Consultant limited, da kamfanin Kama Integrated Services limited da kuma BRMFB, sun kara horar da Matasan Yankin Jihar Borno ta Arewa da ta Yamma har su kimanin 200 harkar Agency Banking da kuma basu horo na musamman akan shirin Babban bankin kasa (CBN) akan harkar e-Naira. Taron horarwar na musamman wanda aka shirya shi na…
Read MoreKwastam Ta Kama Fetur Na Miliyoyi Ana Yunkurin Fitarwa Waje
Hukumar Kwastam da ke ya?i da fasa kwabri ta ?asa ta ce ta kama man fetur da ya kai kimanin lita 81,425 da ake shirin fita da shi daga ?asar. Hukumar ta ce ta kama man fetur ?in a Badagry da ke Legas da kuma kan iyakar Najeriya da Jamhuriyyar Benin. A wani sa?o da hukumar ta kwastam ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce an ?ura man fetur ?in cikin duro-duro kusan 60 sa’annan aka saka wani man a cikin buhuna da ku ma jarkoki. Hukumar ta ce…
Read MoreGwamnatin Borno, Bizi Mobile, Kama Integrated Da BRMFB Sun Horar Da Matasa Shirin e-Naira
Daga Wakilinmu A kokarinsu na ganin sun samarwa da Matasa ayyukan yi, Gwamnatin Jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Zulum, da hadin gwiwar kamfanin hada hadar kudi irin na zama ni, wato Bizi Mobile Cashless Consultant limited, da kamfanin Kama Integrated Services limited da kuma BRMFB, sun horar da Matasan Jihar Borno Maza da Mata har su kimanin 270 harkar Agency Banking da kuma basu horo na musamman akan shirin Babban bankin kasa (CBN) akan harkar e-Naira. Taron horarwar na musamman wanda aka shirya shi na yini biyu, ya gudana…
Read MoreAna Satar Danyen Mai Na Dala Miliyan 700 Duk Wata A Najeriya – NNPC
Babban Manajan Kamfanin NPMS, reshe daga kamfanin fetur na ?asa, NNPCL, Bala Wunti, ya ce a duk wata ana satar ?anyen mai a?alla ganga 470,000 a ?asar nan. Wunti ya yi wannan bayani lokacin da ya ke rangadin duba kadarorin NNPCL. Ya ce an ?iyasta ?anyen man da ake dacewa ?in duk wata zai kai na dala miliyan 700. Sannan ya ce rabon da bututun mai na Bonny Terminal ya yi aiki tun cikin watan Maris, saboda ?arayin ?anyen mai masu fasa bututu. Ya ce wannan matsala ta haifar wa…
Read MoreAn Sake Bankado Zunubban Abba Kyari
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ta banka?o wasu kadarori 14 mallakar tsohon shugaban rundunar tattara bayanan sirri ta hukumar ‘yan sandan kasar DCP Abba Kyari. An ruwaito cewa kadarorin sun hadar da manyan kantunan sayayya, da gidaje, da filin wasan polo, da filaye tare kuma da gonaki. An zargi Kyari da kin bayyana kadarorin nasa dake wurare daban-daban a birnin Tarayya, Abuja da birnin Maiduguri na jihar Borno. An kuma gano sama da naira miliyan 207 da euro 17,598 a asusun ajiyarsa…
Read More‘Yan Sanda Sun Fara Cin Gajiyar Sabon Albashi
Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ta ce ta fara biyan Jami’an ‘yan sandan kasar sabon tsarin albashi da ta gyara musu. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ranar Alhamis a shafinta na Tuwita. Tun a cikin watan Nuwambar 2020 ne gwamnatin kasar ta yi alkawarin inganta tsarin albashin jami’an ‘yan sandan kasar. Dama dai ‘yan kasar da dama, da ma su kansu ‘yan sandan sun sha korafe-korafen cewa albashin da gwamnatin kasar ke biyansu ya yi…
Read MoreDa Dumi-Dumi: An Nada Yayan Aisha Buhari Shugaban Kamfanin Buga Kudi
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Ahmed Halilu a matsayin Manajan-Darakta na kamfanin buga ku?i na ?asa. Halilu, wanda yayan uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ne, ya ri?e kamfanin a matsayin rikon kwarya bayan murabus din Abbas Masanawa a ranar 16 ga watan Mayu. An jiyo daga majiya mai ?arfi cewa shugaban ya amince da na?in ne bisa shawarar gwamnan babban banki na kasa, Godwin Emefiele, wanda ke rike da mukamin shugaban hukumar NSPMC. Halilu…
Read MoreAn Samu Ribar Mai Ta Biliyan 799 A Farkon Shekarar Bana – Babban Banki
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban bankin ?asa CBN ya ce kasar ta samu ribar Naira biliyan 799.10 a bangaren albarkatun man fetur a rubu’in farko na shekarar 2022. Alkaluman sun nuna raguwar ribar da kashi 28.3 cikin dari, idan aka kwatanta da ribar tiriliyan 1.11 da aka samu a rubu’in karshe na shekarar 2021. An ruwaito daga majiya mai tushe cewa ku?in tallafin da kasar ta biya a rubu’in farkon ya kai biliyan 675. Ribar man fetur din dai ya hadar da ribar…
Read MoreNeman Mafita: Za Mu Sayar Da Kadarorin Gwamnatin Tarayya – Ministar Kudi
Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya zata karbi sabon bashin sama da Naira Triliyan 11 tare da sayar da dukiyoyin gwamnati don kasafin kudin 2023. Ta bayyana cewa gwamnati zata bukaci kudi N12.42 Trillion idan har zata cigaba da biyan tallafin mai a 2023. Hajiya Zainab ta bayyana hakan ne ranar Litnin yayinda ta bayyana gaban yan majalsar wakilai a birnin tarayya Abuja. Ta yi bayanin cewa zabi biyu gwamnati ke da shi, na farko…
Read MoreNNPC Ta Zargi Masallatai Da Majami’u Da Satar Danyen Mai
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kamfanin Man Fetur na ?asa NNPC ya zargi jami’an gwamnati, malaman addini, hukumomin tsaro da ma wasu ma’aikatanta da hannu wurin satar danyen mai a kasar. Da ya ke magana a wurin taron tawagar shugaban kasa karo na 49 a gidan gwamnati a Abuja, Shugaban NNPC, Mele Kyari ya ce dukkan rukunin mutanen kasar na da hannu a laifin. Ya bayyana cewa duk lokacin da aka samu kayan satar a masallatai da coci-coci, akwai wasu masu barnata kayan gwamnati…
Read MoreNeja: Hukumar Wutar Lantarki Ta Yanke Wutar Gidan Gwamna
Labarin dake shigo mana daga Minna babban birnin jihar Neja na bayyana cewar Kamfanin Abuja Electricity Distribution Company watau AEDC masu raba wutar lantarki a jihar sun datse wutar gidan Gwamnati da ma’aikatun gwamnati. Hakan ya biyo bayan tulin bashi da kamfanin na AEDC yake bin gidan gwamnati, ma’aikatu da hukumomin jihar ta Neja. AEDC sun ba gwamnatin Neja wa’adi ta biya kudin, da abin ya gagara sai aka yanke masu wuta. Kamar yadda jami’in hulda da jama’a na kamfanin AEDC, Mohammed Pele ya shaidawa ‘yan jarida a ranar Juma’a,…
Read MoreAmurka Za Ta Dawo Wa Najeriya Dala Miliyan 23 Da Abacha Ya Kai Ajiya
Gwamnatin Najeriya da Amurka sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar maido da dala miliyan 23 da ake zargin Abacha ya wawure zuwa gida Najeriya. Jakadiyar Amurka a Najeriya Mary Leonard ce ta sanya hannu a madadin gwamnatin Amurka yayin da ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin kasar Abubakar Malami ya rattaba hannu. A nasa jawabin, Malami ya ce matakin mayar da kudaden, ya samo asali ne daga wasu jerin tattaunawa da tarukan da aka yi tsakanin Najeriya da ma’aikatar shari’a ta Amurka da kuma hukumar yaki da laifuka ta kasar…
Read MoreAn Tsawaita Wa’adin Biyan Bashi Ga Kafafen Da Aka Soke Wa Lasisi
Hukumar kula da kafofin ya?a labarai kasa NBC ta tsawaita wa’adin biyan bashin da ta saka wa kafofin labaran da ta ?wace wa lasisi. A ranar Juma’a ne NBC ta ?wace lasisin aiki na kafofin ya?a labaran fiye da 50 saboda abin da ta ce sun kasa biyan bashin da take bin su kuma ta ba su awa 24 su yi hakan. Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, hukumar ta ce ta ?ara wa’adin zuwa ranar Laraba, 23 ga watan Agustan 2022 maimakon kwana ?aya,…
Read MoreSatar Danyen Mai: An Cafke Jirgin Kasar Turai A Najeriya
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jami’an Sojin ruwan Najeriya sun damke wani jirgin ruwa, (MT) HEROIC IDUN, mallakin kamfanin Hunter Tankers AS dake Scandinavia, Norway yana kokarin satar danyan mai a Najeriya. Jami’in tsare-tsare da shirye-shiryen hukumar, Saidu Garba, ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja ranar Juma’a. A cewarsa, jirgin ya shigo Najeriya ne kuma kai tsaye ya nufi rijiyar man Akpo ba tare da izinin kamfanin NNPC ba. Hukumar ta bayyana cewa jirgin ruwan ya isa rijiyar man ne cikin daren…
Read MoreYaki Da Rashawa: Buhari Ba Da Gaske Ya Ke Ba – Naja’atu Muhammad
Sananniyar ‘yar Siyasar nan ta jihar Kano kuma mamba a kwamitin ?auka da ladabtar da ‘Yan sanda Naja’atu Mohammed, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba. An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.…
Read MoreBadakala: EFCC Ta Gayyaci Hadimar Ministan Shari’a
Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta yi wa Ladidi Mohammed, shugaban sashin kwato kadarorin gwamnati na ma’aikatar shari’ar tambayoyi kan zargin bada?alar damfara. Da farko, an tsare Ladidi, wacce ta hannun daman Abubakar Malami, ministan shari’a kuma antoni janar ne, na tsawon kwanaki kan zargin damfara wurin sayar da kayayyakin gwamnati na biliyoyin naira da aka kwato daga ‘barayin gwamnati.’ An bada belinta amma bata cika ka’idojin belin ba sai ranar Alhamis. Amma, majiyoyi sun tabbatar da cewa…
Read MoreTattalin Arzikin Najeriya Na Dab Da Rushewa – Masana
Yayin da Najeriya ke shirin za?en 2023 cikin shekara mai zuwa, hujjoji na ?ara bayyana cewa tattalin arzikin ?asar fuskantar matsanancin yanayi biyu: wato baitilmalin da ba ko ranyo a ciki, sai kuma raguwar da tattalin ke yi a kullum. Jami’an gwamnati da manyan ‘yan kasuwar da ke da masaniyar halin da ake ciki, sun ce ana nuna damuwa sosai a Abuja da Legas, yayin da wani za?a??en jami’in gwamnati ya jawo hankalin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele cewa abin da ya rage a asusun Najeriya da ke waje…
Read More