Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya sake nanata aniyarsa ta janye tallafin man fetur a 2023, yana mai cewa “ba abu ne mai ?orewa ba idan aka yi la’akari da abin da ke faruwa”.
Buhari ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da kasafin ku?in 2023 na naira tiriliyan 20.51 ga gamayyar taron ‘yan majalisar tarayya a ranar Juma’a.
A cewarsa: “Maganar tallafin mai abu ne mai cike da cecekuce a ?asarmu tun daga shekaraun 1980.
“Sai dai, halin da ake ciki a yanzu ya nuna cewa ba abu ne mai ?orewa ba. A matsayinmu na ?asa, dole ne mu tunkari batun nan da tunanin cewa akwai bu?atar mu samar da tsarin kula da sauran ?angarori na al’umma.”
Buhari ya ce dakatar da biyan tallafin ya zama wajibi don samun ku?in gudanar da sauran ayyuka sakamakon ?arancin ku?in shiga.
“Yayin da muke neman fa?a?a hanyoyin samun ku?in shigarmu, dole ne mu mayar da hankali kan yadda za mu alkinta arzikinmu.”
Wannan ne kasafi na ?arshe da gwamnatin Buhari ta gabatar yayin da yake shirin sauka daga mulki a watan Mayun 2023, wanda a lokacin ne gwamnatin ke son daina biyan tallafin.
