Kishin Kasa: Buhari Zai Karrama Tsohuwar Ministar Kudi

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari zai karrama Shugabar ?ungiyar Cinikayya ta Duniya, Ngozi Okonjo-Iweala da lambar girmamawa ta GCON.

Okonjo-Iweala wadda tsohuwar ministar ku?i ce a Najeriya, ta taya ‘yan ?asar murnar cika shekara 62 da samun ‘yancin-kai, inda ta yi amfani da damar wajen gode wa Buhari da ‘yan ?asar.

“Ina godiya ga Mai Girma Shugaban ?asa da ‘yan Najeriya saboda girmama ni da za a yi da lambar GCON,” a cewarta cikin wani sa?on Twitter da ta wallafa a yau Asabar.

GCON na nufin Grand Commander of the Order of the Niger a turance kuma ita ce lambar girma ta biyu mafi girma a Najeriya.

Rahotanni sun ce Buhari zai karrama mutum 437 a bikin da za a yi ranar 11 ga watan Oktoba da lambobi daban-daban, cikinsu har da tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ?asa Abba Kyari, da mawa?i Burna Boy, da Mataimakiyar Sakataren MDD Amina Mohammed.

Related posts

Leave a Comment