Ana Satar Danyen Mai Na Dala Miliyan 700 Duk Wata A Najeriya – NNPC

Babban Manajan Kamfanin NPMS, reshe daga kamfanin fetur na ?asa, NNPCL, Bala Wunti, ya ce a duk wata ana satar ?anyen mai a?alla ganga 470,000 a ?asar nan.

Wunti ya yi wannan bayani lokacin da ya ke rangadin duba kadarorin NNPCL.

Ya ce an ?iyasta ?anyen man da ake dacewa ?in duk wata zai kai na dala miliyan 700.

Sannan ya ce rabon da bututun mai na Bonny Terminal ya yi aiki tun cikin watan Maris, saboda ?arayin ?anyen mai masu fasa bututu.

Ya ce wannan matsala ta haifar wa Najeriya ?arancin ku?a?en shiga, kawo cikas wajen raba man gas da kuma haifar da ?arancin ?anyen man da ake ha?owa.

Haka a ?arshen watan Agusta shi ma Shugaban NNPCL, Mele Kyari ya ce da ha?in-bakin mutanen yanki, shugabannin addinai da jami’an tsaro ake satar ?anyen mai.

Related posts

Leave a Comment