Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya zata karbi sabon bashin sama da Naira Triliyan 11 tare da sayar da dukiyoyin gwamnati don kasafin kudin 2023.
Ta bayyana cewa gwamnati zata bukaci kudi N12.42 Trillion idan har zata cigaba da biyan tallafin mai a 2023.
Hajiya Zainab ta bayyana hakan ne ranar Litnin yayinda ta bayyana gaban yan majalsar wakilai a birnin tarayya Abuja.
Ta yi bayanin cewa zabi biyu gwamnati ke da shi, na farko a cigaba da biyan kudin tallafin mai a 2023 gaba daya ko kuma a biya na watanni shida kadai zuwa bayan zabe.
A cewarta, idan aka biya kudin har karshen shekara, ana bukatar N12.41 Trillion a 2023. Amma idan zuwa watan Yuni bayan zabe za’a biya, N6.72 trillion za’a kashe kan tallafin mai.
Ta kara da cewa da kamar wuya a iya biyan kudin tallafin gaba daya dubi da halin da ake ciki yanzu, amma idan aka biya na watann shida kadai da ‘dan sauki. A cewarta, idan aka biya na wata shida, za’a iya karban bashin N9.32 trillion don cikasa kasafin kudin 2023.
