Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta bai wa kamfanin man NNPC da kungiyar dalilan man fetur ta IPMAN wa’adin sa’o’i 48 su tabbatar da wadatuwar fetur a fadin kasar. Kakakin DSS, Peter Afunanya, ne ya fitar da sanarwar a Abuja bayan ganawar sirri da masu ruwa da tsaki a harkokin fetur. Sanarwar ta ce NNPC ta tabbatar da cewa tana da wadataccen fetur jibge da zai wadatar da ‘yan kasar har bayan bukukuwa karshen shekara. Ya ce an baza jami’an DSS a kowanne kusurwa na kasar domin hukunta duk…
Read MoreCategory: Tattalin Arziki
Tattalin Arziki
Kayyade Cire Kudi: Majalisa Ta Bukaci Babban Banki Da Yin Taka Tsan-Tsan
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu ?an majalisar dattawa sun nuna fargaba game da matakin babban bankin ?asar na ta?aita ku?in da al’umma za su iya cirewa daga asusun ajiya. Shugaban marasa rinjaye na majalisar Phillip Aduda ya janyo hankalin wakilan majalisar kan cewa matakin na CBN zai yi illa ga al’umma musamman ma masu ?ananan sana’o’i. A nasa tsokacin, shugaban majalisar Sanata Ahmed Lawan ya ja hankalin bankin na CBN da ya yi nazari kan lamarin kafin yanke hukunci kai-tsaye, kasancewar matakin zai…
Read MoreBabban Bankin Kasa Ya Takaita Adadin Kudin Da ‘Yan Najeriya Za Su Cire A Bankuna
Babban bankin Najeriya CBN ya fitar da sababbin dokoki na hada-hadar ku?a?e a bankunan ?asar. A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, CBN ya ta?aita yawan ku?ade la?adan da ?an ?asar za su iya cirewa daga asusun ajiyarsu na banki. Wannan sanarwa na zuwa ne mako biyu bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya ?addamar da sabbin takardun naira da aka sabunta. Sabbin matakan da CBN ?in ya fitar a ranar Talata sun ha?a da: Yawan ku?in da mutum ?aya zai iya fitarwa a banki a sati shi ne naira…
Read MoreAl-Mundahana: Buhari Ya Kori Shugaban Hukumar NIRSAL
An tsige Manajan Darakta na Hukumar rarraba tallafi a fannin Aikin Gona na kasa (NIRSAL) daga aikinsa. Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito Majiyar Dimokuradiyya ta nakalto cewa korar Aliyu Abdulhameed, ba zai rasa nasaba da zarge-zargen cin hanci da rashawa da yawa ba. A watan Janairun bana ne Daily Trust ta gudanar da bincike kan yadda NIRSAL ke bayar da lamunin rancen biliyoyin Naira na wasu kamfanoni masu zuba jari don noma hekta 20,000 na alkama na noman rani a Kano da kuma Jigawa bisa zargin karkatar da…
Read MoreEFCC Ta Sake Bankado Zunubban Tsohuwar Ministar Mai
Hukumar EFCC ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa, Diezani Madueke, tsohuwar ministar albarkatun man fetur, ta bai wa ‘yan siyasa dala miliyan 115 domin yin magudin zaben shekarar 2015. Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka a ranar Laraba nan a wani taron karrama sabbin kwamishinonin zabe (INEC) da aka yi a Legas. Bawa wanda ya samu wakilcin Adukwu Michael baban darakta a hukumar mai kula da sashen binciken laifuka, ya bayyana wannan rashin gaskiya da tsohowar ministar ta aikata a matsayin babban abin takaici…
Read MoreCushe A Kasafin Kudi: An Raba Rana Tsakanin Ministar Jin Kai Da Ministar Kudi
Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar batun yi wa kasafin kudin 2023 ciko da majalisar dattawan ke tuhumar ma’aikatar kudi na ci gaba tayar da kura. Kan wannan batun, Ministar jin kai ta aika wa takwararta ta ma’aikatar kudi wata wasika wadda a ciki ta dora alhakin bayyanar wasu naira biliyan 206 cikin kasafin kudin ma’aikatarta, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin wadannan ma’aikatun gwamnatin biyu. A makon jiya, yayin da ministar jin kai ta halarci zaman majalisar dattawa domin kare kasafin kudin ma’aikatarta,…
Read MoreMun Yi Nasara A Shari’o’i Fiye Da 3000 A Bana – EFCC
Hukumar EFCC mai ya?i da cin hanci da rashawa a ta ce ta yi nasara a shari’o’i 3,328 da ta gurfanar da mutanen da take zargi da cin hanci cikin wata 11 na shekarar 2022. Shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa ya zuwa 18 ga watan Nuwamba 2022, sun yi nasarar ?wace ku?i naira miliyan 755 daga hannun tsohon babban akanta na ?asa wa?anda suka mayar wa gwamnati. Kazalika, EFCC ta ?wace kadarorin alfarma uku daga hannun Kanar Bello Fadile (mai ritaya) – tsohon mataimaki na musamman ga tsohon…
Read MoreEFCC Ta Sake Gurfanar Da Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Gaban Kuliya
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna kan wasu zarge-zargen da ke da alaka da halasta kudin haram. Hukumar na zargin tsohon gwamnan tare da wasu mutum uku da karbar cin hancin kudi da suka kai naira miliyan 700 daga hannun tsohuwar ministar albarkatun man fetur Diezani Alison-Madueke domin yin magudin zaben shugaban kasa na shekarar 2015. Sauran mutum ukun da ake tuhumarsu tare da tsohon…
Read MoreBankin Bada Lamuni Ya Nemi A Gudanar Da Bincike Kan NNPC
Bankin Bada Lamuni na Duniya IMF ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kaddamar da bincike akan man fetur din da kamfanin NNPC ya ce ana sha a cikin kasar da kuma irin kudaden tallafin da ake zubawa da sunan talaka. IMF ya kuma bukaci bincike akan kudaden da kamfanin ke zubawa a lalitar gwamnati sakamkon irin gibin da ya gani bayan ziyarar aikin da jami’ansa suka kammala a Najeriya. Hukumar ta ce abin takaici ne yadda kamfanin ke tafka asara sakamakon kashe makudan kudade da biyan dimbin basussuka, yayin da…
Read MoreKotu Ta Wanke Babachir Lawal Daga Badakalar Cire Ciyawa
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta wanke tsohon sakataren gwamnatin tarayya Mista Babachir Lawal da wasu mutum biyar daga zargin wata bada?ala ta ku?i naira miliyan 544. Hukumar ya?i da cin hanci da yi wa tattalin arzi?in ?asa zagon ?asa ta Najeriya, EFCC ce ta gurfanar da mutanen, tana zargin su da almundahana kan wata kwangilar cire ciyawa, wadda ku?inta ya kai naira miliyan 544. Mai sharia’a Charles Agbaza ya ce babu wani abu da zai nuna cewa Babachir yana da laifi a cikin bayanan da shaidu 11…
Read MoreSauya Takardun Naira: Mun Gano Gwamnoni Masu Kuruciyar Bera – EFCC
Shugaban hukumar hana cin hanci da rashawa a Najeriya, Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa, adadin gwamnonin da hukumarsa ke sa ido a kansu bisa zargin tara kudin haram ya karu. Bawa ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, dangane da irin nasarorin da hukumar tashi ta samu. Bawa ya ki bayyana adadin gwamnonin ko sunayensu, inda yace ba ya son a yi masa mummunar fahimta ko a sauya mishi magana. An ce gwamnonin suna kokarin fara fitar da kudaden tare da tabbatar…
Read MoreSauya Takardun Naira: Za A Sanya Idanu Kan Masu Kai Kudi Banki
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministar tattalin arziki, kasafi da tsare-tsaren kudi ta Najeriya, Zainab Shamsuna Ahmed tayi karin haske game da sababbin kudi da za a buga. A wani bayani da aka fitar a shafin LinkedIn a ranar Alhamis, an fahimci ba haka nan za a kyale mutane su rika maida kudin hannunsu cikin bankuna ba, ba tare da sa ido ba musanman daga Hukumar EFCC. Ministar tace za a hukunta duk bankin da ya sabawa ka’idojojin da aka gindaya, Ministar ta bayyana…
Read MoreTashin Dala: EFCC Ta Damke ‘Yan Canji A Biranen Abuja Da Legas
Hukumar Yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, ta kama ‘yan canji 87 a babban birnin kasar Abuja da kuma jihohin Lagos da Kano a ci gaba da kokarin kawo karshen matsalar karanci da tashin farashin Dala da ake fuskanta a kasar. An ruwaito cewar jami’an hukumar EFCC sunyi dirar mikiya a wasu daga cikin wuraren canjin kudi da ke Abuja tare da kama mutane 25 masu gudanar da harkar ta haramtatciyar hanya wanda ya ke zuwa bayan kama wasu 40, adadin da ya nuna cewa mutane 65 ke nan…
Read MoreMun Samu Gagarumar Nasara A Shekarar Bana – EFCC
Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya tayi nasarar daure mutane 2, 847 da suka aikata laifuffukan damfara a shekarar bana. Shugaban EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa ya yi wannan bayani yayin da bayyana a gaban majalisar ?asa bada rahoton ayyukan hukumar. Abdulrasheed Bawa ya zauna da kwamitin yaki da rashin gaskiya na majalisar dattawa domin ya kare kasafin kudin hukumar na shekarar 2022/23. An yi wannan zama ne a bayan labule, sai bayan nan Bawa ya samu lokaci…
Read MoreNuna Kwazo: Bankin Najeriya Ya Karrama Kamfanin Bizi Mobile
Babban Bankin kasa wato CBN, Karkashin jagorancin Shugaban bankin Mista Godwin Emefele, ya karrama kamfanin Bizi Mobile Cashless Consultant limited da lambar yabo a matsayin gwarzon kamfani mafi jajircewa da kwazo akan tallata shirin e-Naira a daukacin kasar baki daya. An shirya bikin karramawar da kuma kaddamar da sabon shirin Babban bankin kasa (CBN) mai taken ‘Digital currency (CBDC) e-Naira.’ wanda ya guda a dakin taro na Eko hotel dake Jihar lagos. A yayin da Shugaban Babban bankin kasa CBN, Mista Godwin Emefel, yake mika kambun lambar yabo ga Shugaban…
Read MoreAdamawa: An Shawarci Gwamnatin Tarayya Da Ba Dillalan Mai Damar Shigo Mai
A wani mataki na magance karancin man fetur a fadin kasan nan baki daya. An sahawarci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta sakarma dillalain man fetur masu zaman kansu mara domin samun damar shigo da mai din. Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar dilalan man fetur mai zaman kanta a Najeriya IPMAN Alhaji Baba-Kano Jada ne yayi wanana kira a zantawarsa da Wakilinmu a Yola. Alhaji Baba-Kano Jada yace mafita daga cikin matsalalolin karanci dama tsadar man fetur a fadin Najeriya ita ce a ba kamfanoni masu zaman kansu lasisin izinin shigo…
Read MoreBankin Najeriya Ya Bada Wa’adin Mayar Da Tsoffin Ku?a?e Bankuna
Sakamakon matakin da babban bankin Najeriya ya dauka na sauya fasalin wasu takardun kudin kasar, an umarci al’ummar kasar da su mayar da tsoffin kudaden da za a sauya zuwa banki. CBN, ya ce idan mutane suka mayar da kudaden ba tare da bata lokaci ba, to za su iya samun musayar kudinsu a kan kari. Ya ce saboda wannan sabon tsarin yanzu an cire duk wani caji da ake yi a kan kudin da ake kai wa bankuna ba tare da bata lokaci ba, kuma duk yawan kudin. To…
Read MoreShugaban Bankin Raya Kasashen Musulmi Ya Ziyarci Najeriya
Shugaban Bankin Raya ?asashen Musulmai IsDB, Dr Muhammad Sulaiman Al Jassar ya kai ziyara Najeriya. Dr Jassar ya fara ziyarar aikin ta kwanaki uku ne a ranar Lahadi 23 ga watan Oktoba. Lokacin ziyarar, shugaban bankin gana da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, zai kuma gana da Ministar Kudin da kasafi ta Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed, domin tattauna batutuwan da suka shafi bunkasar tattalin arziki. Al Jassar yana ziyarar ne tare da manyan abokan hulda daga ciki har da, Bankin kasa da kasa na bunkasa fannin noma a Afirka.…
Read MoreBa Mu Dakatar Da Samar Da Iskar Gas Ba – NLNG
Kamfanin samar da iskar gas na girki a Najeriya, Nigeria LNG Limited (NLNG), ya musanta rahotannin da ke cewa ya dakatar da aiki a wasu masana’antunsa da ke kudancin ?asar saboda ambaliyar ruwa. Cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na Twitter, NLNG ya ce dukkan masana’antunsa na aiki “duk da cewa ba yadda suka saba ba saboda ?arancin gas da yake fuskanta daga abokan hul?arsa”. Tuni aka shiga fargabar hauhawar farashin gas ?in saboda tsoron ?arancinsa a kasuwa bayan kamfanin ya ba da sanarwar rage yawan gas…
Read MoreBabban Bankin Kasa Ya Sanar Da Sayar Da Bankin Polaris
Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban bankin Najeriya, CBN, ya sanar da kammala sayar da Bankin Polaris, wanda rikici ya kunno kai a kwanan nan. Daraktan sashin hulda da al’umma na hukumar babban Bankin ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Abuja. Nwanisobi, ya sanar da cewa CBN da AMCON ne suka jagoranci sayar da bankin ga wadanda suka fi yawan hannun jari a bankin da sunan ‘Strategic Capital Investment Limited’ (SCIL). Sanarwar…
Read More