Satar Danyen Mai: An Cafke Jirgin Kasar Turai A Najeriya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jami’an Sojin ruwan Najeriya sun damke wani jirgin ruwa, (MT) HEROIC IDUN, mallakin kamfanin Hunter Tankers AS dake Scandinavia, Norway yana kokarin satar danyan mai a Najeriya.

Jami’in tsare-tsare da shirye-shiryen hukumar, Saidu Garba, ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja ranar Juma’a.

A cewarsa, jirgin ya shigo Najeriya ne kuma kai tsaye ya nufi rijiyar man Akpo ba tare da izinin kamfanin NNPC ba.

Hukumar ta bayyana cewa jirgin ruwan ya isa rijiyar man ne cikin daren 7 ga Agusta da niyyar satar mai amma jami’anta suka dakilesu. Yace: “Sakamakon bincike, NNPC ya bayyana cewa ko kadan bata baiwa jirgin izinin diban danyen mai ba.”

“Hakan yasa aka tura jami’an sojin ruwa na NNS GONGOLA washegari don bincikan abinda ya kai jirgin Akpo.” “Matukin jirgin ya bayyana cewa lallai basu da izinin diban mai a wajen.”

Saidu Garba ya cigaba da cewa sakamakon haka suka umurci direban jirgin ya jira sai NNPC ya bashi izini, amma Direban ya kurewa jirginsa gudu kuma ya nufi kasar Sao Tome daga baya aka damke jirgin ruwan a kasar Equatorial Guinea bayan kure masa gudu.

Related posts

Leave a Comment