An Tsawaita Wa’adin Biyan Bashi Ga Kafafen Da Aka Soke Wa Lasisi

Hukumar kula da kafofin ya?a labarai kasa NBC ta tsawaita wa’adin biyan bashin da ta saka wa kafofin labaran da ta ?wace wa lasisi.

A ranar Juma’a ne NBC ta ?wace lasisin aiki na kafofin ya?a labaran fiye da 50 saboda abin da ta ce sun kasa biyan bashin da take bin su kuma ta ba su awa 24 su yi hakan.

Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, hukumar ta ce ta ?ara wa’adin zuwa ranar Laraba, 23 ga watan Agustan 2022 maimakon kwana ?aya, inda ta umarce su da su biya ku?in.

“Dukkan kafofin labaran da suka gaza biyan bashinsu, an umarce su da su kulle daga ranar 24 ga Agusta, 2022,” a cewar sanarwar da shugaban hukumar Balarabe Shehu Ilelah ya sanya wa hannu.

Related posts

Leave a Comment