El-Rufai Ya Kashe Kaduna Fiye Da Yadda Ake Zato – Henry Marah Sakataren Kwamitin Binciken El-Rufai

images (76)

An bayyana tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i a matsayin wata annoba da ta fa?a wa Jihar Kaduna a tarihin kafuwar jihar, bisa la’akari da yadda tsohon Gwamnan ya yi wa Jihar rugu-rugu da tarin basussuka na fitar hankali.

Mai magana da yawun Kwamitin da Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa domin bincikar bada?alar ku?a?e da tsohon gwamna El-Rufa’i ya yi, Honorabul Henry Marah ya bayyana haka, a yayin tattaunawarshi da ‘yan jaridu a ofishin sa na majalisar dokokin jihar Kaduna.

Honorabul Henry ya kara da cewar a binciken da kwamitin nasu ya gudanar kan tsohon Gwamnan ya banka?o yadda El-Rufai ya yi amfani da damar da ya samu na mu?amin gwamnan ya yi wa jihar Kaduna tatas tamkar babu gobe da tulin bashi wanda ake kashe mu raba tsakanin tsohon Gwamnan da abokanansa.

?an Majalisar wanda ke wakiltar mazabar karamar hukumar Jaba a majalisar, kuma shine shugaban kwamitin kula da harkokin yada labarai na majalisar yace baya ga tarin ku?i Naira Biliyan 423 da Gwamnan ya yi watanda dasu, da akwai wasu ?arin ku?a?e har Naira miliyan 600 da aka fitar dasu a rana guda aka buga sharholiya dasu tsakanin wasu shafaffu da mai mutanen tsohon Gwamnan.

Honorabul Henry ya bada misali da wani na hannun daman tsohon Gwamnan mai suna Jimmy Lawal, wanda yake da tarihin cin amanar wasu ?asashen duniya kuma aka sanar da nemansa ruwa a jallo sai gashi abin mamaki, El-Rufai ya ?auko wannan mutumin ya ?a?aba wa jama’ar jihar Kaduna.

“Babban abin takaici shine dukkanin mutanen da El-Rufai ya ?auko suka taimaka mishi wajen ruguza jihar Kaduna ba ‘yan jihar Kaduna bane, halazalika bama ‘yan Arewa bane, mutane ne daga kudancin Najeriya wanda hakan ya sanya ko ka?an ba sa jin tausayin jama’ar jihar Kaduna wajen kashe Jihar da bashi’

Sakataren Kwamitin binciken yace a halin yanzu sun kammala aikin da aka ?ora musu na bincike kuma sun banka?o ba?a?en macizai marasa imani da suka yi tarayya wajen talauta jihar Kaduna, sannan sun mi?a rahotonsu ga mai girma Gwamna Uba Sani, sannan sun mi?a wa hukumar EFCC da ICPC, abin da ya rage yanzu shine za su jira su ga matakan da za a dauka na gaba.

Henry Marah ya kuma godewa jama’ar jihar Kaduna bisa goyon bayan da suka basu ta hanyar sa su a addu’o’i inda ya bada tabbacin za su yi tsayuwar daka wajen ganin dukiyar jama’ar jihar Kaduna da aka daka ma wasoso ta dawo garesu.

Related posts

Leave a Comment